Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya jaddada kudiri...
Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya jaddada kudirin jami’ar na samar da ingantaccen ilimi.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a taron karawa juna sani na kasa da kasa karo na farko kan “Binciken Bayanai, tushe domin rubutun Ilimi: Nasiha da Dabaru” wanda dakin karatu na Jami’ar ya shirya a ranar Asabar, 2 ga Yuli, 2022.
Taron na yini biyu wanda aka gudanar ta hanyar Intanet, an gudanar da shi ne a makarantar kimiyyar kiwon lafiya, wanda ya samu halartar dalibai, malamai da sauran wadanda aka gayyata daga sassan duniya.
Ya ce shawarar kafa MAAUN ya samo asali ne daga hangen nesan wanda ya kafa Jami'ar da kuma jajircewarsa na samarwa duniya shugabanni masu ilimi da hazaka ta hanyar samar da ingantaccen ilimi ta hanyar samar da shi da sauki da kuma samu ga kowa.
A cewarsa, jami’ar ta fara ayyukan ilimi da makarantu hudu da suka hada da Makarantar Kimiyyar Koyon Zamantakewa da Gudanarwa, Makarantar Kwamfuta, Makarantar Kimiyyar Likitanci da Makarantar jinya.
Farfesa Israr ya ce jami'ar, wacce ta kasance daya daga cikin mafi kyawun jami'o'i masu zaman kansu a Afirka, za ta yi kokarin bunkasa ilimi da fasahar kere-kere a yankin hamadar Saharar Afrika da ma kuma fiye da hakan wacce ba ta da misali a nahiyar Afirka.
Ya kuma kara da cewa, kafa Jami'ar MAAUN ya bunkasa harkokin kasuwanci a jihar Kano.
Shugaban MAAUN ya godewa wadanda suka shirya wannan bitar tare da yin kira ga mahalarta taron da su yi amfani da damar da aka ba su yadda ya kamata domin bunkasa iliminsu da fasaharsu.
A jawabinsa a wajen taron, mataimakin shugaba kan harkokin gudanarwa/rajistira, Dakta Habib Abubakar Uwais ya ce akalla mahalarta taron da suka yi rijista ba su gaza kasa da 1185 inda ya nuna cewa sama da rabin wadanda suka yi rijista suna bibiyar taron ta Intanet.
Dakta Uwais, ya bayyana yadda za a bayar da takardar shaidar ta 'E-certificate' na taron, sannan ya bukaci mahalarta taron musamman, dalibai da su yi amfani da ilimin da suka samu domin babu wata jami'a da za ta ci gaba idan dakin karatunsu ba ya aiki kuma ba tare da kayan zamani ba.
Ya taya daliban murnar samun damar halartar taron sannan ya bude soma taron.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Kodineta/Ma'aikacin Laburaren, Dakta Ukashatu Hamza, ya ce manufar shirya taron ya samo asali ne daga sha'awar masu ruwa da tsaki na dakin karatu na bunkasa basirar dalibai da sauran mahalarta kan dabarun neman bayanai ta yanar gizo da kuma sabon salo na rubuce-rubucen ilimi domin fuskantar kalubalen dake cikin duniyar ilimi.
Ya shawarci malamai da dalibai da su ci gajiyar wannan bitar domin tsarin laburare na jami’ar ya tsaru wajen tallafa musu domin cimma manufofinsu.
Ya kuma kara da cewa "Duniyar dakunan karatu ta samu sauyi na asali don haka muna bukatar mu amince da wannan sabon tsari ko kuma lamarin zai tilasta muku yin amfani da shi."
An gabatar da takardu a taron bitar wanda shi ne irinsa na farko da dakin karatu na Jami’ar ta shirya.
No comments