Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, ta nada mataimakin shugaban Jami’ar Tarayya dake Dutsin...
Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, ta nada mataimakin shugaban Jami’ar Tarayya dake Dutsinma (FUDMA), Farfesa Armaya’u Bichi, a matsayin memba a majalisar gudanarwarta.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na FUDMA, Malam Habib Umar-Aminu ya fitar a ranar Asabar a Katsina.
Ya bayyana cewa nadin na Bichi ya biyo bayan taron kwamitin amintattu na MAAUN, wanda aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Shugaban Majalisar Gudanarwa kuma wanda ya kafa Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo, a lokacin da yake taya wanda aka nada murna, ya ce zabin nasa ya biyo bayan binciken kwakwaf da aka yi a tsakanin fitattun mutane dake da hazaka da jajircewa wajen bunkasa ilimi da ci gaban dan Adam.
“Zabinka ya kasance saboda waÉ—annan halaye, musamman ma Æ™warewarka a fannin ilimi. Ka karÉ“i sakon taya murnata da gaisuwata,” mai magana da yawun ya ruwaito Gwarzo yana cewa.
No comments