Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kwankwaso ya zabi Fasto Idahosa a matsayin mataimakinsa

Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar New Nigeria People's Party, NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zabi F...



Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar New Nigeria People's Party, NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zabi Fasto Bishop Isaac Idahosa a matsayin matamakinsa a zaben 2023.

Jam'iyyar ta NNPP ce ta sanar da wannan labarin a shafinta na Tuwita ranar Alhamis.

Fasto Bishop Idahosa dan asalin Jihar Edo ne da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar na NNPP Bishop kuma babban fasto na Cocin God First Ministry, wadda aka fi sani da Illumination Assembly, Lekki Light Centre (LLC) a birnin Lagos.

No comments