Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Nijer Ta Gargadi Dalibai Kan Wata Takardar Bogi Da Ake Yadawa A Kafafen Sada Zumunta

Hukumar gudanarwa na Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN) ta nesanta kanta dangane da wata takarda bog...



Hukumar gudanarwa na Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN) ta nesanta kanta dangane da wata takarda bogi da ake yadawa a kafafen sada zumunta inda ake bukatar dalibai da su sayi "sabbi da kuma nagartaccen wayoyi". 

A wata sanarwa da mai magana da yawun MAAUN Kano, Tukur Muntari ya fitar a ranar Asabar ya shawarci daliban da su yi watsi da takardar domin ba daga hukumar jami'ar ta fito ba. 

"An jawo hankalin Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN) kan wata kirkirarriyar takarda wacce aka ce ta fito ne daga ofishin Rajistira na MAAUN Nijer wanda wani Abubakar Adamu, jami'in tsangaya ya sanyawa hannu kan bukatar dalibai su sayi sabbin waya da kuma wayoyin da aka kara musu inganci, muna mai sanar da ku cewa wannan takardar ta bogi ce. 

A don haka Jami'ar har wala yau na shawartar dalibai musamman masu karantar kimiyyar kwamfuta da su yi watsi da takardar wacce aka sanyawa kwanan watan 22/07/2022 tare da lambar tantancewa ta MAAUN/CY/1098. 

Ana kuma shawartar dalibai da su kasance masu bibiyar labari domin tabbatar da sahihancinsa.

No comments