Daga Fatima Idris Zariya A cikin wannan satin ne Dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar Sabon Gari Honorabul Ali Baba daga Jam&...
Daga Fatima Idris Zariya
A cikin wannan satin ne Dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar Sabon Gari Honorabul Ali Baba daga Jam'iyyar PDP ya bai wa mutane 300 tallafin karatun kwamfuta wato na'ura mai kwakwalwa.
Taron yaye daliban dai an gudanar da shi ne a dakin taro na Events Center dake kan titin Sokoto Road Sabon Garin Zariya.
Wakilinmu ya sami halartar wannan taro ga rahoton da ya turo mana.
Bayan da jiga-jigan Jam'iyyar PDP na karamar hukumar ta Sabon Gari suka kammala zuwa tare da dukkan daliban da aka bai wa horon ne sai aka bude taron da addu'ar kamar yadda aka saba.
Bayan an yi addu'a ne sai aka gabatar da manyan baki Sarakuna da Malaman addini da sauran masu fada aji a jihar Kaduna da karamar hukumar ta Sabon Garin.
Bayan an tabbatar da kowa ya natsu ne sai aka yi jawabin dalilan taro.
Haka zalika an gabatar da daliban su 300 a gaban manyan baki don su shaida da kokarin Dan majalisar na su ya yi.
Tuni jama'ar da suka sami halartar wajen suka dauki tafi da jinjina ga Dan majalisar ganin yawan daliban da suka samu horo musamman a bangaren kwamfuta don tunkarar ci gaban zamani.
Wadannan dalibai sun hada maza da mata ne cikin har da matan Aure.
Bayan gabatar da irin nasarorin da aka samu ne ta bakin Kodinetan koyarwar mai suna Dan Malam Hakazalika Malamin ya gabatar da nasarori masu yawan gaske da wannan tsarin ya samu.
Bayan haka sai aka bai wa mawaka da masu wasan kwaikwayo damar nuna bajintarsu ga dimbin mutanen dake zaune a wannan zaure.
Da aka kammala shakatawa ne sai aka mikawa dalibai takardun shaidarsu ta hannun Sarakuna da limamai dake wannan waje.
Wakilimmu ya sami zantawa da Honorabul Ali Baba Dan majalisar na jihar Kaduna a Jam'iyyar PDP wanda shi ne ya dauki nauyin wannan horon ga mutane 300.
Honorabul Ali Baba ya fara ne da godiyar Allah madaukakin sarki bisa nasarar da ya samu a wannan rana .
Haka zalika ya yi godiya ga dukkan Malamai da Sarakuna da suka sami halartar wannan taron yaye daliban da ya dauki dauyin koya masu ilmin na'ura mai kwakwalwa wato kwamfuta.
Kuma ya ce hakan somin tabi ne ga jama'arsa da ikon Allah.
Dan majalisar ya bayyana ire-iren kalubalen da ya fuskanta tun farkon hawansa kujerar da yake.
Ya ce akwai shari'o'i da ya fuskanta da dama amma cikin ikon Allah ya sami nasara akan su wanda sune suka yi ta kawo masa tarnaki akan aikin ci gaban dake zuciyarsa inda ya yi alwashin zai ci gaba da bayar da kulawa ta bangaren ilmi sosai da ikon Allah.
Karshe ya yi kira ga daliban da su yi kokari a bangaren da suka sami horon da amfanar al'ummarsu.
Ya yi horo da zaman lafiya da tabbatar da kowa ya je ya karbi katin zabe don zabo mutanen da za su wakilce su a ko wanne mataki.
Ya yi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.
No comments