Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matsalar Tsaro: Malam Bello Yabo Ya Yi Wa Buhari Nasiha Mai Ratsa Zuciya

Daga Malam Bello Yabo Yakamata ka ji tsoron Allah Muhammadu Buhari. Yakamata ka ji tsoron Allah. Wannan bushewar zuciya taka ta ...


Daga Malam Bello Yabo

Yakamata ka ji tsoron Allah Muhammadu Buhari. Yakamata ka ji tsoron Allah. Wannan bushewar zuciya taka ta yi yawa. Wannan rashin tausayi na ka ko dai ak kai Fir'auna Buhari ai iyakar abin da za ka iya yi ke nan. Iyakar abin da za ka yi ke nan na rashin tausayi.

Wannan bushewar zuciya taka Buhari ta yi yawa, ka ci amanarmu. Ka ci amanarmu, ka san irin wahalar da muka yi a kanka, ashe ka san busasshiyar zuciya gareka. Ba ka da imani, ba ka da tausayi. Duk mai imani yana barin mutane cikin wannan tasku? Tunda ba 'ya'yanka bane. Ga mata, wasu da goyo da kananan yara cikin wannan tasku, cikin wannan bala'i, kuma gwamnati ta kawo ido ta saka musu; wacce irin gwamnati ce wannan? Wanne irin mutane ne ya ku jami' an gwamnati. Yakamata ku ji tsoron Allah. Muna yi muku nasiha ku ji tsoron Allah. Zukatanku sun bushe da yawa.

Ya ya za ku iya fuskantar Ubangiji da hakkin BayinSu da kuka yi banza da shi? Ya za ku iya fuskantar Ubangiji?

Rantsuwa da kuka yi kai Buhari, kana Musulmi aka baka Kur'ani ka yi rantsuwa za ka yi adalci, yanzu wadannan ka yi musu adalci? A kama su kana da yadda za ka yi ka kwato su amma ka kyale su. Don haka ku ji tsoron Allah ya ku shugabannin gwamnati. Ku tausaya ma wadannan Bayin Allah.

Yanzu ya ya za ku ji a ce matanku ne da 'ya'yanku da' yan'uwanku aka kama?

Yanzu Buhari da a ce matarka ce aka kama, matarka ce a cikin halin da wadannan matan ke ciki, ya za ka ji? To duk yadda za ka ji, haka nan 'yan'uwan wadannan bayin Allah suke ji. Yakamata ku tausaya musu.

Ku sani ba nan za a dawwama ba. Sannan wallahi Annabi sallallahu alaihi wasallama ya fadi, Hadisi ya tabbata, kuma kowa ya san da hadisin; hadisi ne mashahuri, Manzon Allah ya ce kowannenku makiyayi ne, kuma kowannenku abin tambaya ne ga abin da aka ba shi kiwo.

-Inji Baban Asma'u, Malam Bello Yabo.

©AMR

No comments