Daga Yusuf Hamisu A ranar Talata ne 12 ga watan Zulhijja Zauren Muryar Matasa na Facebook ya gabatar da taron Gani da Ido karo n...
Daga Yusuf Hamisu
A ranar Talata ne 12 ga watan Zulhijja Zauren Muryar Matasa na Facebook ya gabatar da taron Gani da Ido karo na 4 a garin Kaduna.
Taron wanda ake shiryawa duk shekara domin sada zumunci da juna, mutane daga sassan Nijeriya da suka hada da Kano, Katsina, Zamfara, Adamawa, Kaduna, da sauran su n suka halarci taron.
Ibrahim Musa da Halliru Abubakar Dabai suka jagoranci taron, inda da farko an bude taron da addu'a, sannan kowa da ya halarci taron ya gabatar da kanshi ta bayyana sunan shi, garin da yake da kuma sunan da yake amfani da shi a kafar sada zumunta ta Facebook. Sai jawabin Maraba daga Bakin Aliyu Dan Hausa.
A cikin jawabin nasa ya nuna jindadinsa da yadda mutane suka halarci taron daga wurare daban-daban, sannan ya yi kira da hadin kai da rashin nuna bambanci, ya kara da yin addu'a Allah ya kawo ci gaba ga wannan gida da kuma kauda matsalar da za ta rinka bullowa don rusa ci gaban gidan, sannan ya yi addua'ar Allah ya maida kowa gidansa lafiya.
Daga nan sai wanda ya kirkiro Group din, Founder Shamsuddeen Saed Muaz ya gabatar da takaitaccen jawabi akan 'Group' din da manufofinsa da abin da ake so a cimmawa.
Daga nan ne shugaban zabe na gidan Hassan Muhammad Rafin Dadi ya tumbuke shuwagabannin da adadinsu ya cika, inda ya jinjina masu da kuma kira gare su da su ci gaba da ba wannan gida gudunmuwar da suka saba. Sai Kuma Mataimakin shi Mallam Yusuf ya rantsar da sabbin shuwagabanni da aka zaba inda ya yi kira a gare su da su yi aiki tukuru domin ciyar da zauren gaba ya zarce inda yake a yanzun.
Daga nan Ciyaman mai jiran gado Hasanul-Mujtaba Khamees ya kaddamar da sabbin ministocin da za su taya shi aiki, da kuma bayyana wasu shirye-shiryen da zai dora zauren ya tafi akan shi.
Bayan wannan an dan shakata da wakar da Hassan Rafin Dadi ya rera da harshen larabci da kuma wacce Real Asas Dan Matashi ya rerawa group din sannan aka raba Satifiket ga shugabannin da suka sauka, da karrama wadanda suka yi nasara a gasar rubutun da aka saka a kwanakin baya, da membobi da official da suka nuna jajircewa tare da karrama wasu da lambar karramawa da girmamawa (awards) saboda gudunmawarsu ga zauren, da Kuma karramawar musamman ga membobin Muryar Matasa a reshen Jihar Kaduna yadda suka yi fice a dukkan jihohin da kuma yadda suka tsara taron.
Daga cikin Manyan bakin da suka halarci taron, Malam Sabiu Pillars a cikin Dan gajeran Jawabin da ya yi, ya bayyana jindadinsa da yadda ya ga ake yin zumunci tsakanin membobin group din da kuma kira da cewa a daure a hakan.
Shima a nasa bangaren Alhaji Aminu Dogo ya nuna matukar al'ajabinsa na yadda ya ga mahalarta a kusan wurare sun halarci taron inda ya ce a zatonsa ya dauka a Kano, Katsina da Kaduna ne kawai mahalarta suka zo, sai ya ji cewa hadda Adamawa, Zamfara da sauran wurare, sannan ya kara da cewa yadda ya ga jama'a na fara'a da murna da ganin juna abin ya kara ba shi dadi da kuma kira ga cewa lallai Matasa sune kashin bayan al'ummar nan, idan har suka hada kansu to za su yi maganin duk wani zalunci da ake yi ko ake ganin yana afkuwa a kasar nan.
A nasa jawabin tsohon Dan takarar Kansila na Unguwar Kanawa/Hayin banki Hon. Yusuf Shagiwa ya nuna farin cikin shi kuma shima ya zama memba a wannan zaure daga yau, kuma zai bada duk wata gudunmawa, kuma ya yi kira ga 'yan siyasa da masu mulki da su rinka tallafama wadannan matasa da gurbin karatu da sana'o'in da za su dogara da kansu su taimaki kansu da kuma 'yan'uwansu.
An yi walima da kayan makulashe, sannan a lokaci guda Membobin Muryar Matasa a reshen Jihar Kaduna sun gabatar da wata 'yar Tamsiliyya Mai darasi sosai domin fadakarwa ga jama'a sannan kuma an kara nishadantuwa da wata wakar da Ussy Kd ya yi, da kuma shahararriyar wakar nan ta bakandamiyar Muryar Matasa "Ni na gaisheku Muryar Matasa Group Zauren Shakuwa, sada zumunta har nishadi a Facebook banga Misalinsu ba".
An yi addu'ar rufewa sannan aka fita waje aka yi hoton bai daya, sannan kowa ya kama hanyar komawa gida.
No comments