Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sallar Idi: Dan Takarar Gwamnan PDP A Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Ya Yi Kira Da A Zauna Lafiya

Daga Bello Hamza Dan takarar gwamnan Jihar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP,  Dr. Dauda Lawal ya yi kira ga daukacin al’...Daga Bello Hamza

Dan takarar gwamnan Jihar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP,  Dr. Dauda Lawal ya yi kira ga daukacin al’ummar musulmi da su zauna lafiya.

Dauda Lawal wanda shi ne shugaban kamfanin Credent Capital LTD, kuma tsohon Shugaban babban bankin nan na First Bank ya yi wannan kira ne bayan kammala sallar idin bana.

Lawal ya gudanar da sallar ne a filin Idi na Zawiyya a garin Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Sheikh Ibrahim Halifa Zawiyya ne ya jagoranci Sallar Idin ta bana, inda hori al’umma da su yi tarayya wurin hidimtawa Nijeriya ba tare da la’akari da bambancin da ke tsakani ba.

Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan idar da sallar, Dauda Lawal ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su hada kai, su kuma rungumi zaman lafiya. 

“Musamman bisa la’akari da halin da wannan jiha tamu ke ciki, muna bukatar zaman lafiya da hadin kai.”

Dandazon masoya da al’umman gari ne suka yi tururuwa suna jinjinawa dan takarar na PDP, Dauda Lawal jim kadan bayan kammala sallar.

No comments