Daga Abubakar M Taheer Sanatan Jigawa Ta Gabas Barrister Ibrahim Hassan Hadejia Ya Ƙaddamar da gasa ga daliban yankinsa Masu haz...
Daga Abubakar M Taheer
Sanatan Jigawa Ta Gabas Barrister Ibrahim Hassan Hadejia Ya Ƙaddamar da gasa ga daliban yankinsa Masu hazaƙa.
Gasar da aka fara ta Ranar Asabat aka ƙarƙare ta ranar Lahadi, ta samu halarta dimbin Al'umma daga sassa daban-daban na masarautar Hadejia, wanda suka haɗa da Malaman makarantu,dalibai,'yan siyasa, masu sarauta dss.
Da yake jawabi yayi bada kyautuka Sanatan Jigawa ta Gabas Barrister Ibrahim Hassan Hadejia, ya bayyana wannan a matsayin wata hanya da za'a dawo da martabar ilimi da sanin muhimmancinsa a wannan yankin.
Ya kara da cewa mun tanaji kyaututtukan kamar Keke -Napep,Babura, Firji,Kekunan hawa,Kekunan dinki dss.
Wanda daliban da sukayi nasara zasu tafi dashi ga Iyayensu, hakan zai kara muku kwarin gwuiwar turo 'ya'yan nasu makaranta.
Barrister Ibrahim Hassan ya kuma gabatar da bada tallafin karatu (Scholarship) ga dalibansa da suka yi nasara dama bude asusun tallafawa Dalibai marasa karfi 'yan Asalin yankin.
Mun kulla Yarjejeniya da bankin NIRSAL wanda zamu bude asusun ajiya ga kowane dalibai inda zamu dauki nauyin karatunsa tun daga inda yake har ya zuwa jami'a.
Haka kuma Sanata Ibrahim Hassan ya bayyana cewa ƙofa a bude take ga sauran 'yan siyasa, masu hannu da shuni, masu Madafin iko dama sauran al'umma kan bada nasu gudunmawa domin samar da ilimi shine gina al'umma.
A karshe Sanata Ibrahim Hassan ya yabawa Malaman makarantun da daliban suka fito inda yace nan gaba kaɗan zai kaddamar da irin wannan gasa ga Malamai masu hazaƙa a makarantun su.
Dayake jawabi A madadin Uban Kasa Mai martaba Sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje CON Wanda ya Sami wakilcin Galadiman Hadejia Alhaji Usman Abdulaziz ya yabawa sanatan Kan wannan namijin kokari nasa wajen zaburantar da yara da iyayensu Muhimmancin neman ilimi.
Inda ya kara da cewa suna neman gwamnatin Jigawa ta sake bude makarantun kimiyya na kwana (Boarding) domin irin bajintar da suka nuna a wajen gasar.
Da yake jawabin Godiya mataimakin gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Dan Modi a madadin Gwamnan jihar, Ya godewa Sanatan bisa wannan namijin ƙoƙarin nasa, inda yace wannan aiki na gwamnatin Jihane Sanata ya rage musu nauyi.
Dan Modi ya kara da cewa dalibanmu na Jigawa musamman na karkaka Allah ya hore musu kaifin basira wajen gane karatu wannan tasa muke alfahi da Dalibanmu a ko'ina.
Mataimakin Gwamnan yayi kira ga sauran 'Yan siyasa da su kwafi irin wannan aiki domin ilimi shine gaba da komai a rayuwa.
A karshe Yayi alkawarin zakulo malaman makarantun da suka koyar da daliban suka fafata a gasar domin gwamnatin ta musu karrama ta musamman.
Bayan Kammala taron an wuce gurin raba kyaututtukan inda Babbar Sakandire Science Kafin Hausa ta zo na farko wanda suka sami kyautar Keke Napep guda 3.
Science Kaugama tazo na biyu wanda aka basu kyautar Babur guda uku.
Na uku a rukunin Sakandire Birniwa wanda suka samu kyautar Firji guda 3.
A rukunin da karamar Sakandire Science Kafin Hausa ne suka zo na farko wanda suka samu kyautar Babura 3 sai Birniwa take bimata wanda ta samu kyautar Firji 3 na karshe sune Hadejia suka sami kyautar keken dinki 3.
A rukunin firamare 'yan aji (4,5,6) Hadejia ce ta daya wanda suka sami kyautar Babura 3 sai Bulangu a mataki na 2 inda suka sami kyautar Firji 3 sai Guri tazo na uku inda suka sami kyautar keken dinki 3.
No comments