Shekara Guda Da Sakin Shaikh Zakzaky: Manjo Hamza Almustapha Ya Ziyarcesa A Abuja


Tsohon Dogarin shugaban Nijeriya, Manjo Hamza Almustapha ya kaima Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibrahim Zakzaky ziyara a gidansa dake birnin Tarayya Abuja.

Shekara guda ke nan da Malamin ya fito da matarsa daga gidan yari tun bayan kisan da sojoji suka yi ma mabiyansa a Disambar 2015 a Zariya. 

Almustapha jigo ne cikin manyan kasar nan da ta bayyana ya fara kai wa Malamin ziyara suka tattauna bayan fitowar Malamin daga gidan Yari.

Manjo Hamza Almustapha yana daga cikin 'yan takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2023 mai gabatowa. 

Post a Comment

0 Comments