Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shugaban Karamar Hukumar Faskari Musa Ado Faskari Ya Yi Kira Ga 'Yan Siyasa

      Hon. Musa Ado Faskari, Shugaban Karamar Hukumar Faskari jihar Katsina .  Daga Awwal Jibril 'Yankara Shugaban karamar h...

     Hon. Musa Ado Faskari, Shugaban Karamar Hukumar Faskari jihar Katsina


Daga Awwal Jibril 'Yankara

Shugaban karamar hukumar Faskari a jihar Katsina Honorabul Musa Ado Faskari
ya yi kira ga 'yan Siyasa da su yi koyi da irin halin Injiniya Samaila Mu'azu Bawa Faskari na Tallafawa 'ya'yan gajiyayyu da Marayu domin su ma su samu Ilimi kamar yadda 'ya'yan kowa suke yi suma.

Ya yi wannan kiran ne a lokacin bikin ba yara 117 'ya'yan Marayu da gajiyayyu da 'yan hijira wadanda aka tsin-tsinto a fadin  karamar hukumar ta Faskari a jihar Katsina wanda kungiyar Injiniya Dakta Samaila Ma'azu Bawa mai yaki da rashin zuwa makaranta ta dinka ma yara 117 
 kayan Makaranta (Uniform) a ranar Litinin 4/7/2022 a dakin taro na makarantar Tsohuwar Makarantar Firamare ta garin Faskari a jihar Katsina. 

Hon. Musa Ado Faskari ya kuma kara da cewa nan bada jimawa ba, karamar Hukumar ta Faskari za ta yi doka kan rashin zuwa makaranta da hana gararamba yara lokacin Karatu.

Shugaban na karamar hukumar ta Faskari Hon. Musa Ado Faskari ya ce kafin zangon karatu na gaba su ma za su tsinto akalla yara dubu daya da dari biyar su yi musu kayan makaranta Insha Allah, inji shi. 

Da yake nasa jawabin a wurin taron, shugaban Hukumar Ilimin bai daya na Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina, Malam Sani Mudassiru ya bada umarnin kar wani shugaban makarantar Firamare a fadin karamar hukumar Faskari, ya sake korar wani dalibi ko daliba daga makaranta don rashin kayan makaranta (Uniform). 

    Malam Sani Mudassiru Faskari, Shugaban Hukumar Ilimin Bai daya na karamar Hukumar Faskari. 

 Ya kara da cewa abin da kawai za a yi shi ne a rubuto masu sunayen yaran da ba su da kayan makaranta su sun dlsan kokarin da za su yi a kan hakan, Inji Shugaban Hukumar Ilimin na bai daya na karamar hukumar Faskari, Malam Sani Mudassiru Faskari. 

Shima ana sa jawabin, Shugaban Malaman tsohuwar Makarantar Firamare ta garin Faskari, Malam Haruna Jibril ya yaba ma namijin kokarin da Injiniya Samaila ke yi ne, ya ce kodayake ba wannan bane karo na farko.

Mutane ne da dama suka samu halartar taron. 
 
Daukacin 'yan majalisar karamar hukumar ta Faskari, shuwagabannin sassa na ma'aikatar Ilimin bai daya na karamar huhumar Faskari, Iyaye da Dalibai da dama sun samu halarta. 

No comments