Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Alhaji Adamu Aliyu Sarkin Kifi Ya Zama Sarkin Samarin Gombe Na Farko A Masarautar Gombe

Daga Idris Fatima Zariya Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III a ranar Lahadi 31 ga watan Yulin J2022 ya t...Daga Idris Fatima Zariya

Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III a ranar Lahadi 31 ga watan Yulin J2022 ya tabbatar ma Alhaji Adamu Aliyu da Sarautan Gargajiya a Matsayin Sarkin Samarin Gombe na farko a Masarautar Gombe dake jihar Gombe.

An haifi Alhaji Adamu Aliyu ne a shekarar 1993. Ya yi karatunsa na addinin Musulunci kamar yadda tsarin al'adar Fulani yake a Arewacin Nijeriya sannan ya yi karatun zamani L. E. A PRIMARY School Bolari Gombe 2002 Zuwa 2008, Govt Secondary School Junior zuwa Senior 2008 to 2011. Bayan kammala Secondary sai ya wuce zuwa Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi Daga 2014 zuwa 2018 Computer Science, 

Adamu Aliyu ya fito daga zuri'ar gidan Sarkin Kifin Gombe 'da ne sajen Alhaji Aliyu Sarkin Kifi, Allah ya azurta shi da son al'ummar jusamman matasa kamar yadda ya tashi ya gani a gidansu wajen hidimar al'ummar. Kuma ya kasance dan kasuwa mai kishin matasan jihar Gombe. 

Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III. Ya ce sun yi Sarautar Sarkin Samarin Gombe ne saboda kyakkyawar alakan shi ga Masarautar Gombe da matasan jihar Gombe wajen kokarin shi na ciyar da al'ummar gaba da kokarin tattalin zaman lafiya da kyautata mu'amular zamantakewar ga hakuri da tawakkali da zumunci saboda haka muna kara kira gare shi da ya ci gaba da dukkan halayyarsa na alheri Allah ya kama.

Bayan tabbatar da shi Alhaji Sama'ila a matsayin Sarkin samarin Gomben ya yi jawabin godiya ga mai martaba sarkin Gwamben da sauran al'ummar da suka bayar da gudummawa kamar haka.

Da Sunan Allah Ubangijin talikai, tsira da Aminci su kara tabbata ga fiyayyyen Halitta Annabi Muhammadu (S.A.W). Muna mika sakon godiyarmu ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Gombe Alh (Dr) Abubakar Shehu Abubakar III da, 'Yan Majalisar Masarautar Gombe.
Allah ya saka masu da alherinsa bisa amincewansu a gare mu. 

Muna Amfani da wannan daman muna godiya mara adadi bisa nuna mana soyayya da zumunci da aka yi na samun karuwan arziki da mu yi abun da muka gada na arzikin sarauta Sarkin Samarin Gombe. 

Lallai Mun ga soyayya kwarai musamman daga cikin gida da abokan mu na nesa masu Albarka inda muka samu addu'ar 'yan'uwa da ma zumuntan mu. Muna kara mika sakon godiya da bangajiya ga dukkan mahalarta wannan Babban al'amari a gare mu mungode kwarai. 

Haka zalika muna kara godiya ga sauran jama'a da suka yi mana addu'ar da kuma wanda suka kira mu a waya. Mungode kwarai Allah ya yi maku sakayya da abin da yake ma ma'abota zumunci. Ameeeeeen

Allah ya ja xamanin Sarki Amin. An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments