Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An kama wani dalibi dan shekara 18 bisa yunkurin yin garkuwa da shugaban makaranta

Jami’an Hukumar Tsaron Al'umma ta Nijeriya (NSCDC),  reshen jihar Neja sun kama wani ɗalibi ɗan shekara 18 da haihuwa, bisa ...


Jami’an Hukumar Tsaron Al'umma ta Nijeriya (NSCDC),  reshen jihar Neja sun kama wani ɗalibi ɗan shekara 18 da haihuwa, bisa zargin yunkurin yin garkuwa da Shugababn Makarantar Koyon Noman Kifi a Sabuwar Bussa.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASC Nasir Abdullahi, ya fitar a yau Laraba.

Ya ce wanda ake zargin, wanda dalibin kwalejin ne, ya haɗa baki da wani mutum ɗaya, wanda a halin yanzu, ya rubuta wasikar barazanar yin garkuwa da provost idan ya kasa biyan kudin fansa.

Sai dai Nasir ya ce wanda ake zargin bai bukaci wani adadi na musamman ba kafin jami’an tsaro su kama shi.

Kakakin ya kara da cewa, nan take aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata babbar kotun majistare kan laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma razanarwa.

No comments