Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ɗan Uwa ko ka Taɓa jin Labarin Ambasada John Mamman Garba?

Sunansa John Mamman. Sunan mahaifinsa Garba Katsina. Kakanninsa sun riƙe sarautar Ƙauran Katsina kafin lokacin Jahadi.  Shine ɗa...Sunansa John Mamman. Sunan mahaifinsa Garba Katsina. Kakanninsa sun riƙe sarautar Ƙauran Katsina kafin lokacin Jahadi. 

Shine ɗan Arewa na farko da ya karanci tattalin arzikin ƙasa wato Economics. Ya samu digirin sa na Economics ne daga ƙasaitacciyar makarantar nan da ake kira London School of Economics.

Shine ɗan Nijeriya na farko da ya riƙe muƙamin Executive Director a Bankin Duniya (World Bank) dake birnin Washington DC.

Yana cikin ma'aikatan farko na ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Nijeriya tun sadda aka buɗe ta a shekarar 1950.

Shine ya fara buɗe ofishin jakadancin Nijeriya dake Amurka. Yana Amurka a lokacin da Nijeriya ta samu ƴancin kai ranar ɗaya ga watan Oktoba 1960, a nan suka yi walimar murnar samun ƴanci.

John Mamman Garba ya riƙe muƙamin Ambasadan Nijeriya a ƙasashe biyar 👉Amurka da Italiya da Girka da Cyprus da Andalus (Spain).

Kamar yadda muka sha faɗi muna nanatawa, a ƙasar nan kullum so ake a nuna Bahaushe bai isa ba. Duk inda Bahaushe yayi fice, ko dai a kore masa hausancinsa ko a naƙasa asalinsa ko kuwa ayi ƙoƙarin binne tarihin sa. 

Anyi ƙoƙarin binne tarihin Ambasada John Mamman Garba.

Ba titi ko layi ko gini ko cibiyar nazari ko ɗakin karatu dss da aka sanya wa sunan sa don tunawa da shi. 

Mun san mafi yawancin masu karatun wannan rubutun, sai yanzu suka fara jin sunan wannan Bawan Allah. 

Amma Allah cikin ikonsa Ya ba Ambasada Mamman Garba damar rubuta tarihin rayuwar sa da kansa cikin wani littafi mai shafi kusan 400 da ya sawa suna THE TIME HAS COME ... wanda kamfanin wallafa littafai na Spectrum ya buga. 

Ambasada Mamman Garba ya koma ga mahaliccin sa a shekarar 1989 kafin littafin da ya rubuta ya fito daga ɗab'i, yana da shekaru 70 a duniya. Akwai ƴaƴa da jikokinsa a Wusasa ta Zaria inda ya yi rayuwar sa.

Muna alfahari da Ambasada John Mamman Garba.

© Nigerian Bahaushe

No comments