Ana ƙirga ƙuri’u a Kenya


Yanzu haka ana ci gaba da ƙirga ƙuri'u a Kenya, don gano sabon shugaban da zai maye gurbin Uhuru Kenyatta.

Wakilin BBC ya ce a zubakan baya an rika samun tashin hankali, amma a bana an jefa kuri'a lami lafiya, sai dai ba a samu fitowar jama'a sosai ba.

'Yan Kenya sun ƙagu su san wane ne sabon shugaban nasu, tsakanin tsohon Firanminista Raila Odinga da ya samu goyon bayan Shugaba Uhuru Kenyatta, ko kuma mataimakin Kenyattan wato William Ruto.

Post a Comment

0 Comments