Daga Wakilinmu MADOGARA ta labarto cewa; a daren jiya, da misalin karfe 12 wani mutumin garin Matseri da ya yo gudun hijira zuw...
Daga Wakilinmu
MADOGARA ta labarto cewa; a daren jiya, da misalin karfe 12 wani mutumin garin Matseri da ya yo gudun hijira zuwa Yankara, ya hallaka mahaifiyar matarsa.
Matar wadda ke dauke da tsohon cikin da likitoci suka sanar da cewa tagwaye ne, ta gamu da ajalinta sakamakom sarar da surukin nata ya yi mata da adda.
Majiyarmu ta shaƙo cewa, mutumin (wanda ya yi kisan) ya hallaka surukar tasa ne saboda ta hana shi bikon matarsa.
A wata majiya kuma an ce, mutumin ya hallaka surukar tasa ne saboda zargin da take yi masa na yunkurin cefanar da 'ya'yansa.
An samu nasarar cafke mutumin a garin Sheme lokacin da yake kokarin guduwa don barin gari.
An yi jana'izar matar, bayan gwaje-gwajen hukuma.
Ya zuwa tattara wannan rahoto, ba mu samu labarin yadda aka yi da mutumin ba.
A lokacin farmakin da magidancin ya kai, an jiyo matarsa tana yekuwar neman taimakon al'umma, inda take cewa "ku taimake ni, mijina zai kashe innata".
Halin firgici da rashin tsaron da ake fama da shi a garin ya hana kowa leƙowa domin kawo mata gudunmuwa.
No comments