Buhari Na Neman A Tallafa Wa 'Yan Pakistan Da Ambaliya Ta Ɗaiɗaita

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da ambaliyar ruwa "mafi tsanani" a tarihin ƙasar Pakistan, yana mai nema wa ƙasar tallafi daga hukumomin duniya.

Wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ambaliyar ta kashe mutum fiye da 1,000 tare da lalata gidaje da tituna da gadoji.

"Shugaba Buhari ya ce 'yan Nijeriya na ci gaba da taya 'yan Pakistan da addu'a yayin da suke fuskantar wannan bala'i mai girman gaske," a cewar Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ƙasa.

Buhari ya roƙi Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin agaji su taimaka wa "jama'ar da ruwa ya raba da muhallansu" da kuma "tallafa musu da abinci yayin da miliyoyi ke buƙatar agaji".

Post a Comment

0 Comments