Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilan Da Ya Sa Masu Aikin Makabarta Ke Yajin Aiki A Abuja

  Ma’aikatan makabarta wadanda kuma ke kula da tsaftar muhalli a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja sun yi barazanar rufe daukacin makab...

 


Ma’aikatan makabarta wadanda kuma ke kula da tsaftar muhalli a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja sun yi barazanar rufe daukacin makabartun da ke karkashin kulawar gwamnati a birnin sakamakon rashin biyan su albashi.

Ma’aikatan sun rufe makabartar Gudu da ke birnin na Abuja kafin daga bisani su bude ta a safiyar wannan Alhamis bayan sun sha matsin lamba daga fadar shugaban kasa.

Fusatattun ma’aikatan sun ce, sun dauki matakin ne domin nuna bacin ransu kan gazawar gwamnati da ta ki cika musu alkawarin karin albashi kamar yadda yake a tsabon tsarin da aka bullo da shi.

Shugababan gamayyar kungiyoyin ma’aikata fararen hula, Kwamared Mukhtar Bala ya ce,  ko da yake sun amince su bude wasu makabartun yanzu haka, amma nan kusa za su garkame daukacin makabartun birnin na Abuja muddin aka gaza cika musu alkawarin da gwamnati ta yi musu.

Bala ya ce, suna fuskantar hatsurra da dama da ke barazana ga lafiyarsu a yayin kula da gawarwakin da aka watsar da su.

Muna kula da gawarwakin da suka shafe tsawon shekaru 3 zuwa 4 a asibitoci duk da cewa, ba mu san abin da ya yi sanadiyar ajalinsu ba.” Inji Bala

No comments