Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Da Iran Sun Kulla Yarjejeniya Kan Makamashin Hasken Lantarki, Man Fetur, Da Na Iskar Gas

Daga Zaharadden Sirajo Abbas Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Honorabul Salisu Iro Isansi ɗan majalisar wakilai ta ƙasa mai wa...


Daga Zaharadden Sirajo Abbas

Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Honorabul Salisu Iro Isansi ɗan majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar birnin Katsina, ya jagoranci tawagar 'yan majalisa zuwa ƙasar Iran, domin tattaunawa akan abin da ya shafi tattalin arziki, tsaro, diplomasiya da karfafa zumunci akan majalisun biyu.

Tattaunawar ta wakana cikin nasara akan abubuwan masu amfani don amfanar da ƙasashen guda biyu. 

A halin yanzu sakamakon ziyarar, kasashen Iran da Nijeriya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna domin fadada hadin gwiwar dake tsakani a fannonin makamashi daban-daban.

Ministan mai na Iran Javad Oji da karamin ministan mai na Nijeriya, Timipre Sylva ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Tehran a ranar Asabar.

Honorabul Salisu Iro Isansi, shi ne ya wakilci karamin ministan man na Nijeriya zuwa Iran din. 

Salisu Isansi wanda ya ziyarci Tehran da  manyan tawagarsa ya samu tarba daga Oji a wurin ma'aikatar mai domin tattauna hanyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Daga cikin alfanun ziyar ya hada da; fitar da ayyukan fasaha da injiniya zuwa Nijeriya, hada hannu da kamfanonin Nijeriya wajen kera motoci masu amfani da mai guda biyu, yin amfani da karfin Nijeriya a fannin samar da iskar gas (LNG), bunkasa rijiyoyin mai da iskar gas na Nijeriya da sake ginawa da gyara matatun man Nijeriya na daga cikin fannonin haɗin gwiwar da aka sanya hannu a kai. 

Da yake jawabi a taron, Oji ya yi tsokaci kan irin karfin da Iran da Nijeriya ke da shi a fannin makamashi, ya kuma bayyana fatan sanya hannu kan irin wadannan sauye-sauyen zai ba da damar kara hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya jaddada cewa Iran da Nijeriya na da dimbin arzikin man fetur da iskar gas kuma Nijeriya ce kasa ta shida da ke fitar da LNG a duniya.

A nasa bangaren ministan na Nijeriya bisa wakilcin Salisu Isansi ya jaddada cewa Iran da Nijeriya sun yi hadin gwiwa sosai a tsakanin kasashen biyu bisa tsarin kawancen OPEC, JECF, da OPEC+, yana mai cewa: “A yau, an sanya hannu kan wata yarjejeniya mai kyau tsakanin kasashen biyu kan batun musayar fasahohin zamani".

Honorabul Salisu Iro Isansi shi ne ɗan majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar birnin Katsina a jam'iyyar APC, sai dai zaben da za a fafata na 2023, bai samu tikitin tsayawa takara ba a jam'iyyar ta APC. Inda tuni jam'iyyar APC a jihar ta Katsina ta bai wa Honorabul Sani Danlami tikiti tsayawa takarar dan Majalisa mai wakiltar birnin ta Katsina, lamarin da wasu fashin bakin siyasa a jihar ke cewa APC ba ta yi kyan kai ba kuma kamar ta cakawa kanta wuka ne. 

Wadansu bayanai da Jaridar MADOGARA ta samu na nuni da cewa Honorabul Salisu Iro Isansi wanda a halin yanzu yake kan kujerarsa ya fi cancanta duba da iliminsa da kwarewarsa da kuma ci gaban da ya kawo sabanin wanda aka bai wa tikitin, Honorabul Sani Danlami, inda wasu ke zargin cewa ma ba shi da kwarewa da kuma ilimi da har zai iya kawowa wadanda yake wakilta ci gaba idan ma ya ci zabe.

No comments