Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Abubakar Gwarzo Ya Yi Wa Oumou Sangare Ta'aziyya Bisa Rasuwar Mahaifiyarta

Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), dake Maradi, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika sakon ta...

Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), dake Maradi, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika sakon ta'aziyyarsa ga fitacciyar mawakiyarnan 'yar Mali, Oumou Sangare bisa rasuwar mahaifiyarta, Aminata Diakite.

Diakite ta rasu ne a Daoud Abougou, yankin Commune V dake Bamako a kasar Mali sakamakon rashin lafiya, kuma an bizne ta ne a ranar Litinin 8 ga watan Agustan 2022 a Madinadiassa, Yanfolila.

Sakon ta'aziyyar na kunshe a wata sanarwa da Farfesa Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Alhamis.

Farfesa Gwarzo wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwar MAAUN Nijeriya, ya bayyana rasuwar Aminata Diakite a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalanta ba, amma ga kafatanin al'ummar Mali da ma Afrika baki daya.

Ya kuma bayyana Marigayiyar a matsayin mahaifiya jajirtacciyya kuma mai aiki tukuru wacce ta kasance 'yar kasuwa domin kula da' 'ya'yanta hudu.

"A madadin Hukumar Gudanarwar Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijar, ina mika ta'aziyyarmu ga Oumou Sangare, 'yan'uwa da abokan arziki da kuma masoyan fitacciyar mawakiyar.

"Hukumar jami'ar na kuma jajantawa gwamnatin Mali bisa wannan babban rashi da aka yi.

Farfesa Abubakar Gwarzo ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayiyar, ya jikanta ya sanya ta a Aljannar Firdausi, sannan ya kuma bai wa Sangare juriyar rashin nan da ba za a iya maida shi ba.


No comments