Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Gwarzo ya bayar da Gudunmawar Naira Miliyan Daya Ga Dalibar Da Ta Fi Kwazo A Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano

Wanda ya assasa kuma shugaban majalisar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ...


Wanda ya assasa kuma shugaban majalisar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan daya ga Maimuna Umar Zarewa, dalibar da ta fi hazaka a Jami’ar North West dake Kano, (a yanzu ana kiranta da Yusuf Maitama Sule University).

Zarewa, ta kammala da matakin farko (First Class) a digirinta na farko a bangaren sinadarai (Chemistry) daga tsohuwar jami'ar Northwest University dake Kano a shekarar 2017. Haka kuma ta samu irin wannan nasara a matsayin daliba mafi hazaka a matakin digirinta na biyu (MSc) a sashen sinadarai na Jami'ar Bayero Kano, inda kuma ta samun gurbin karatun digiri na uku (PhD) kyauta a kasar Saudiyya.

Da yake sanar da bayar da tallafin, Farfesa Gwarzo ya yaba wa Zarewa bisa nasarorin da ta samu tare da jaddada muhimmancin saka hannun jari ga matasa masu fasaha irin Zarewa.

Ya kuma bai wa wacce ya bai wa tallafin takardar shaidar kwarewa domin zaburantar da sauran dalibai wajen fuskantar karatunsu da dukkanin hazaka. 

Ya bayyana Zarewa a matsayin daliba mai hazaka, ƙwazo da amfanarwa, wanda burinta na samun ingantaccen ilimi, idan aka tallafa mata, hakan zai ba ta damar cimma burinta a rayuwa.

Farfesa Gwarzo ya bayyana cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kowacce kasa, yana mai nuni da cewa idan da Nijeriya za ta bai wa bangaren fifiko, da kasar ta kasance daya daga cikin kasashen da suka ci gaba.

Da take mayar da jawabi, Maimuna Umar Zarewa ta yi godiya ga Farfesa Gwarzo bisa wannan karamcin da ya yi mata, inda ta kara da cewa babu wanda ya bayar da gudunmawa wajen neman iliminta, idan ka cire iyayenta kamar Farfesa Gwarzo.

Ta bayyana cewa, wanda ya kafa Jami'ar shi ne mutum daya tilo da ya samo mata aiki a Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma, kuma a lokaci guda ya taimaka mata wajen samun gurbin karatu na digiri na uku a kasar Saudiyya.

Ta kuma godewa wadanda suka shirya wannan taron, inda kuma ta shawarci sauran daliban Jami’ar da su fuskanci karatunsu da kwazo domin samun nasara a rayuwa.

An haifi Maimuna Umar Zarewa a ranar 11 ga watan Maris, 1995 a Kano, kuma ta yi makarantar Firamare ta Zarewa Central inda ta kammala a 2006. Ta kuma halarci makarantar Ruby Springfield College dake Maiduguri daga nan ta wuce tsohuwar Jami'ar Northwest University a Kano (A yanzu ana kiranta da Yusuf Maitama Sule University, Kano) kuma ta kammala a 2017.

Zarewa ta yi Digiri na biyu (Msc) a Physical Chemistry a Jami’ar Bayero Kano, kuma a halin yanzu tana karatun digirin digirgir (PhD) a fannin Physical Chemistry a Jami’ar King Fahad of Petroleum and Mineral Resources dake Saudi Arabia.

Ta kasance mai koyarwa ce na ɗan lokaci a Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nigeria dake Kano a 2022, kuma Lakcara ce a Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma daga 2020 zuwa yau.

Ta kasance memba a kungiyoyi da dama kuma ta sami takardun shaida da kyaututtuka daban-daban.

No comments