Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Haziƙar Yarinya Mai Shekaru 11 Ta Samu Tallafin Karatu Bankin Duniya Na AGILE

Yarinya ƴar asalin jihar Kano mai shekaru 11, Saratu Garba Dan’Azumi, wacce take da baiwar lissafi, ta sami tallafin karatu daga...


Yarinya ƴar asalin jihar Kano mai shekaru 11, Saratu Garba Dan’Azumi, wacce take da baiwar lissafi, ta sami tallafin karatu daga Bankin Duniya, karkashin shirin AGILE.

Yarinyar wacce take aji 4 a firamare, ta dai na zuwa makaranta shekara ɗaya da ta wuce, ta ce ta sami damar iya lissafin ne bisa taimakon malamin lissafinta.

“ ƴan ajin mu suna kirana da ‘Turrum’ shi isa na daina zuwa makaranta, saboda bana son sunan,” in ji ta.

Yayin da jaridar Daily Trust ta kaiwa yarinyar ziyara a wani kauye da ke Ƙaramar Hukumar Gaya, an jarraba yarinyar da tambayar cewa idon da ta kai shekara 30 a duniya, kwana nawa tayi a duniya kenan, nan take ta amsa da cewa kwana 10,800, sanan aka kara mata da wasu tabbayoyin duka ta ansa su dai dai.

No comments