Hukumar gudanarwar ta Jami’ar Maryam Abacha American University dake Nijer (MAAUN), ta taya shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed B...
Hukumar gudanarwar ta Jami’ar Maryam Abacha American University dake Nijer (MAAUN), ta taya shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai.
Jamhuriyar kasar Nijar ta samu 'yancin kai ne a ranar 3 ga watan Agustan shekarar 1960.
Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaba kuma wanda ya kafa Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wacce aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Laraba.
Farfesa Abubakar Gwarzo wanda shi ne ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke Kano, ya yi amfani da wannan damar wajen taya al’ummar Jamhuriyar Nijar murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai.
“A yayin da jamhuriyar Nijar ke bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai, a madadin hukumar gudanarwa na jami’ar ina taya daukacin ‘yan kasar ta Nijar murnar wannan gagarumin biki,” inji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Ya roki Allah madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa Shugaba Mohamed Bazoum jagora domin ci gabantar da kasar.
Ya kuma bayyana shugaba Bazoum a matsayin babban jigo kuma mai kishin kasa wanda ya nuna himma wajen ci gaban kasarsa tun bayan zabensa a watan Afrilun bara.
Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar jami’o’i masu zaman kansu na Afrika (AAPU), ya bukaci ‘yan Nijar musamman ma matasa da su shiga duk wata sana’a mai ma’ana domin su ba da ta su gudummawar domin ci gaban kasarsu.
No comments