Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Juya min magana a kai, ban ce zan bai wa jihohi ragamar jami'o'in gwamnatin tarayya ba -Atiku

Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyar  PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai miƙa wa gwamnatocin jihohin kasar ragamar tafiyar...Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyar  PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai miƙa wa gwamnatocin jihohin kasar ragamar tafiyar da jami'o'in gwamnatin tarayya ba.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar ya ce sun lura cewa an juya maganar da ɗan takarar shugaban kasar na PDP ya yi a wajen wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a Legas a kan batun da ya shafi bangaren ilimi da hanyoyin da zai bi wajen warware matsalolin da bangaren ke fuskanta.

Ya ce a cikin bayanan Atiku, bai ce zai mika ragamar kula da jami'in gwamnatin tarayya ga jihohi ba idan har aka zabe shi a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Wannan ba daidai ba ne don bai hadi haka ba a lokacin da yake bayar da amsa a kan tambayoyin da aka yi masa game da manufofinsa in ji shi.

Ya ce abin da Atiku Abubkar yake nufi shi ne matakan da zai bi daki-daki na rage wa gwamnatin tarayya nauyin tafiyar da jami'on da ke karkashinta.

A don haka batun cewa zai mika wa gwamnatocin jihohi raga,ar tafiyar da jami'oi ba gaskiya ba ne.

No comments