Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kasurgumin Dan Fashin Daji, Aleru Ya Kwato Ma Mutanen 'Yankara Shanunsu

Daga Wakilinmu Ga alama sulhun da aka yi tsakanin mutanen Yankara ta karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina da babban barawon ...


Daga Wakilinmu

Ga alama sulhun da aka yi tsakanin mutanen Yankara ta karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina da babban barawon dajin nan na jihar Zamfara ya fara aiki. Domin kuwa a ranar Asabar 30/7/2022 wajen misalin karfe 8 na safe, wasu ‘Yan bindigar Daji su ka yi awon gaba da wasu shanun, Alhaji Umaru Salisu, daya daga cikin limaman garin ‘Yankara.


 Lamarin ya auku ne a gabashin garin na ‘Yankara, inda anen Alhaji Umaru suka je huda, suna cikin yin hudar ‘yan bindigar suka afka masu suka kwace Shanun.

Su na ji suna gani tilas ‘yan bindigar suka kora Shanun, su kuma suka dawo gida, ganin miyagun bindigogin da suke dauke da su. Haka labarin ya ci gaba da wanzuwa na kwantar Shanun a cikin garin.

Ganin abin da ya faru, sai jagoran garin na ‘Yankara ya kira shugaban ‘Yan bindigar Daji, Adamu Aleru, don shaida masa halin da ake ciki, na karbe masu shanu.

Inda nan take ya tayar da Kwamandojinsa dake kewaye da shi ya ce su bi sawu inda suka kwato shanun daga barayin da suka sace su.

Labarin da majiyar jaridun Katsina City News ke samu an mayar wa da mai Shanun, shanunsa yanzu, kuma jama’ar gari sun ci gaba da shiga Daji domin gudanar da aikin su, biyo bayan dawowar Shanun.

A kwanakin baya ne, mutanen 'Yankara suka gayyaci Adamu Aleru domin zaman sulhu da shi kuma ya yi masu alkawarin zai tsare masu gonakin su su ci gaba na noma har zuwa kwasar amfanin gona.

Kuma har ya zuwa yau bai saba alkawari ba.

©Katsina City News

No comments