Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kisan Ƴan Shi'a Masu Jerin Gwanon Ashura a Zaria: Sannunku Jami'an Tsaronmu Masu Jarumta a Cikin Gari

Daga Comrade Yahaya M Abdullahi Ita jinjina ana yinta ne ga mutumin da ya yi ƙwazo haɗi da Juriya wajen gudanar da aikin da aka ...


Daga Comrade Yahaya M Abdullahi

Ita jinjina ana yinta ne ga mutumin da ya yi ƙwazo haɗi da Juriya wajen gudanar da aikin da aka bashi, an fi son aikin ya zamanto mai kyau wanda zaka yi alfahari dashi a duniya da lahira, wanda ya saka aikin shima yayi alfahari, haka ma Iyalenka da kayi aikin zasu yi alfahari da kai saboda kayi ƙoƙari ka kare musu martabansu wajen gudanar da aiki mai kyau, amma idan kayi akasin hakan na tabbata kai kanka har mutuwarka baza ka taɓa yafe ma kanka ba ballantana kuma Iyalenka in ka bayyana musu irin aikin da ka aikata.

Ranar 10, ga watan Muharram, rana ce da dukkan musulmi na duniya suka bata muhimmanci, wasu ɓangare suna gudanar da bikin cika ciki, ɓangaren ƴan Shi'a kuma a duk faɗin Duniya suna Kuka domin tunawa da abunda ya samu Sayyidana Husaini jikan Manzon Allah, wannan duka wanda yake wannan duniyar yasan hakan na faruwa a dukkan ƙasashen da ƴan Shi'a suke. A shekarar nan ma an gudanar dasu lafiya amma banda a Najeriya, a Najeriyar ma cibiyar arewa wato Jihar Kaduna.

Jami'an tsaro su bayyana da rana tsaka, ba da kayan ƴan Bindigar Daji ba ballantana mu ce ƴan bindiga daɗi ne, ƴan Sanda ne da rana wanda hotuna masu motsi da marasa motsi sun ɗauki hotunansu inda suka bayyana suna harbi kai harma da zagaye yanda kasan sun shiga sansanin ƴan Bindigar da suka shekara biyar suna ƙoƙarin shiga sun ka sai wannan ranar, amma fa duka wannan sun yi ne akan waɗanda ake kira da ƴan Shi'a, wanda su kansu jami'an tsaron da suka yi wannan aika-aika in ka tambayesu dalilin da yasa suka aikata wannan aikin basu da cikakkiyar amsar da zasu baka akan abunda suka aikata, Rayuwar matasa har bakwai sun salwantar ba tare da jin komai a rai ba tare da jikkata wasu da daman gaske, kuma a tunaninsu Allah sai ya bar jinin nan haka kawai, ko wanda ba musulmi ba in ka kashe shi Allah bazai bar jininsa ba ballantana musulmi wanda kawai kuke da saɓanin fahimta, ba Makami ya ɗauka ba ballantana ka ce makami ne a hanunsa.

Jihar Kaduna: a wannan jihar ne fa ake cinikin mutum kamar dilar Gwanjo, a wannan jihar ne fa kake tunanin in ka kai safiya ba lallai ka kai yamma ba ko dare, a wannan jihar ne fa in ka kama hanya zaka je ba tunaninka Haɗarin dake kan hanya ba, tunaninka kuɗin fansar da zaka biya, a jihar da ko me ka mallaka dole ka siyar dashi domin ka kai wa ƴan Ta'adda kuɗin suna daji a zaune, kai kace babu Gwamnati a jihar, ballantana jami'an tsaron da aka dauke su aiki ake biyansu kuɗi domin kare rayukan ƴan ƙasar daga abunda zai je ya dawo kamar ƴan Bindiga da sauransu, to amma sai gashi waɗanda ake so a kashe ba su ake kashewa ba a jihar.

Kullum sai kaji ance maka ƴan bindiga a Jihar Kaduna sun dira wani gida ko wani unguwa sun ɗauki mutane ko sun kashe mutane, aikin kenan, to in dai har jami'an tsaron da ake biya domin su kare mutanen garin nan suma zasu zama suna kashe mutane menene marabansu da ƴan bindigar nan dake daji?

Jaridun Najeriya basu ce komai musamman jaridun da suke magana akan yankin arewa, misali BBC Hausa, Daily Thrust da sauransu ba don komai ba saboda tsoron kada a yanka musu tara, domin a yanzu a Najeriya matuƙar gidan jarida zata fito ta bayyana asalin abunda ke faruwa a ƙasar to fa dole ta shirya ma biyan tara domin ba gaskiyar ake so a faɗa ba iya lissafin kenan, mun ga hakan kurkusan nan akan trust TV da ta bankaɗo ƴan Ta'adda tare da hira dasu, maimakon aji da ƴan ta'addar sai aka dawo kan gidan Jaridar harda yanka mata tara kai gwaɓi.

To Shin Najeriya ina zamu ne, ko kuma in ce yankin Arewa ina zamu je?

Allah ka jiƙan waɗanda aka kashe ka bama Iyayensu dangana akan wannan mummunan ta'addanci da ƴan Bindigar dake cikin gari suka yi. Tir.

No comments