Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwankwaso ya naɗa Kofa da Johnson a matsayin jami'an yaɗa labaran takararsa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya amince da naɗin Abdulmumin Jibrin Kofa da Ladipo Johnson a...


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya amince da naɗin Abdulmumin Jibrin Kofa da Ladipo Johnson a matsayin jami'an yaɗa labaran yakin neman zaɓensa.

Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Kwankwaso, Ibrahim Adamu, ya fitar, ta ce an zabi masu magana da yawun biyu ne saboda kwarewarsu wajen aika sako ya je inda ake so, sadaukarwa ga NNPP, da kuma hanyoyin isar da sako masu yawa.

Yayin da ya ke yaba wa sabbin masu mukaman,  Kwankwaso ya bukace su da su kai sakon jam’iyyar NNPP da yakin neman zabe na RMK2023 zuwa kowane lungu da sako na kasar nan.

 Jibrin dai tsohon dan majalisar wakilai ne, wanda ya kware wajen gudanar da yakin neman zabe da kuma harkokin jama'a.

“Kwararren dan siyasa kuma hazikin mai wayar da kan jama’a, Jibrin ya yi digirin digirgir na BSc, MSc da PhD a Jami’ar Abuja da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya samu ƙware wa a harkokin siyasa da diflomasiyya da harkokin kasa da kasa. Yana da PLD, SEP, da MBA daga Harvard, London da SBS Zurich bi da bi.

Haka shima Johnson, lauya, shi ne manaja a kamfanin lauyoyi na Agbese & Johnson (Legal Consultants) da kuma shugaban Cibiyar Ci gaban Kasuwanci da Gudanarwa ta Afirka.

Shahararren mai sharhi kan al'amuran jama'a kuma tsohon dan takarar gwamna kuma dan takarar majalisar wakilai a jihar Legas,  Johnson ya kammala karatunsa na jami'a a  jihar Legas, LASU.

No comments