Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Ta Taya Farfesa Maigari Murnar Zama Shugaban Jami'ar Northwest Sokoto

  Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer da Nijeriya (MAAUN), ta taya Farfesa Ahmed Maigari Ibrahim murna bis...

 


Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer da Nijeriya (MAAUN), ta taya Farfesa Ahmed Maigari Ibrahim murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin shugaban sabuwar jami’ar Northwest da aka kafa a Sakkwato.

Shugaban na MAAUN na Nijar kuma shugaban Majalisar Gudanarwa ta MAAUN Nijeriya, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya aika da sakon taya murnar ne ga sabon shugaban a cikin wata wasika wacce ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a Kano a ranar Litinin.

Farfesa Abubakar Gwarzo wanda kuma shi ne ya kafa Jami’ar Franco-British International University dake Kaduna, kuma Shugaban kungiyar Jami’o’i Masu zaman kansu na Afrika (AAPU), a madadin Hukumar Gudanarwar Jami’o’in ya yi wa sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar Northwest fatan samun nasara. 

Ya kuma yi masa addu’ar Allah madaukakin Sarki ya yi masa jagora, ya kuma ba shi hikimar jagorantar wannan jami'a. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya bayyana sabon mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Ahmed Maigari Ibrahim a matsayin malami jajirtacce, mai hakuri, da rikon amana wanda zai kawo ci gaba da bunkasa jami’ar ta bangarori daban-daban.

"Muna addu'ar cewa a yayin da ka shiga Ofis, Allah madaukakin Sarki ya taimake ka ya kuma baka nasara," in ji wasikar.

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar ta MAAUN ta bayyana kyakkyawan fatan ta na cewa nadin sabon shugaban jami’ar zai kara wa jami’ar daraja. 

Sabon shugaban Jami'ar sanannen masanin muhalli ne, kuma masani ne wanda ya san sha'anin gudanarwa. A kwanakin baya ne majalisar gudanarwa ta Jami’ar Northwest da ke Sakkwato ta amince da nadin sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar mai zaman kanta. 

Jami’ar Northwest dake Sokoto tsohon gwamnan jihar ta Sokoto ne, Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sokoto) ya kafa ta, kuma tana daya daga cikin jami’o’i masu zaman kansu da aka kafa a jihar Sokoto. 

Hukumar Kula da Jami'o'i ta Kasa (NUC) ta ba da lasisin fara gudanar da aiki a watan Mayun 2022.

No comments