Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mai Martaba Sarkin Kano Ya Kai Ziyarar Ban Girma Jami'ar Maryam Abacha American University Ta Nijeriya Dake Kano

  Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Litinin 8 ga watan Agusta, 2022 ya ziyarci Jami’ar Maryam Abacha Amer...


 Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Litinin 8 ga watan Agusta, 2022 ya ziyarci Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, a muhallinta na dindindin dake Hotoro GRA, a jihar Kano.

Sarkin ya samu tarba daga jami’an Jami’ar da suka hada da, wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, shugaban MAAUN Kano, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr da mataimakin shugaba bangaren gudanarwa, Dr. Habib Awais Abubakar.

Sauran sun hada da Mataimakin Shugaba bangaren gudanarwa na MAAUN Nijar, Dakta Shuaibu Tanko, Daraktan Tsare-tsare da Tabbatar da inganci, Dakta Nura A. Yaro, Farfesa Ibrahim Lawal na Makarantar Kwamfuta da kuma Mataimakin Shugaban Kudi na MAAUN, Mista Dauda Abdulrasaq Kayode da sauransu. 

A yayin ziyarar, Sarkin ya samu rakiyar wasu daga cikin membobin majalisar Masarautar

tare da sauran masu rike da sarauta a masarautar.

A nasa jawabin, Sarkin ya bayyana godiyarsa ga wanda ya assasa MAAUN bisa kafa Jami’ar a Kano wanda ya ce zai taimaka matuka wajen samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan kasa tare da bunkasa harkokin zamantakewa da tattalin arzikin al’ummar jihar.

A yayin ziyarar an zagaya da Mai Martaba wasu wurare da suka hada da dakin kula da kuma makarantar koyon aikin jinya tare da kuma dakin karatu na Jami'ar sannan ya jagoranci sallar Azahar a babban masallacin jami'ar.

Ziyarar ta bai wa Sarkin damar ganin Jami'ar wacce ta fi kowacce jami'a mai zaman kanta ba kawai a Nijeriya ba har ma da Afrika baki daya.


No comments