Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Makasudin fitowarmu muzaharar Ashura - Shaikh Abdulhameed Bello

*Sojoji da 'yan sanda sun afka ma masu komawa gida bayan an tashi muzaharar  Daga Ammar M. Rajab  Kamar yadda aka saba a duk...


*Sojoji da 'yan sanda sun afka ma masu komawa gida bayan an tashi muzaharar 

Daga Ammar M. Rajab 

Kamar yadda aka saba a duk shekara, 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na gudanar da muzaharar Ashura domin juyayi tare da tunatar da al'umma irin kisan gillar da aka yi wa Imam Husaini (AS) da iyalan gidansa da Sahabbansa a filin Karbala a shekara ta 61 bayan hijirar fiyayyen halitta, Annabi (SAWW). 

Muzaharar ta bana a Zariya an fara ta ne da misalin kusan karfe 9 na safe, inda aka kammala ta da misalin karfe 10 da mintoci na safe. Muzaharar wacce aka shafe fiye da awa guda ana gudanar da ita, an fara lafiya, aka kuma kammala lafiya. 

An fara muzaharar ne daga Kofar Doka, inda aka dumfaro Lemu, daga nan aka mika aka nufi Rimin Kwakwa da Rimin Tsiwa har aka iso Babban Dodo. 

Masu muzaharar sun kasance cikin tsari, sanye da bakaken kaya dauke da tutoci da fastoci na alamin dake nuna juyayin ranar Ashura. Suna tafe suna rera baitocin alhini da juyayin kashe Imam Husaini (AS). 

Mahalarta muzaharar wanda ya hada maza da mata, yara da manya, matasa da Dattijai da Tsoffi sun kasance cikin natsuwa a yayin muzaharar. Inda al'ummar gari da dama suka yi dafifi suna kallon masu muzaharar a duk inda aka wuce. 

A yayin zantawarmu da wasu daga cikin a mahalartar muzaharar, sun jaddada mana manufarsu ta fitowa muzaharar a yau Litinin 10 ga watan Al-Muharram, inda suka ce; sun fito ne domin juyayi da kuma alhini tare da tunatar da al'umma irin abin da ya faru da iyalan gidan Manzon Allah (SAWW) a irin wannan rana. "mun fito ne saboda mu nuna bakin ciki akan kisan gillar da aka yi wa Imam Husain (AS). Sakonmu ga al'umma a wannan rana shi ne mu nuna musu irin kisan gillar da aka yi wa Imam Husain sakamakon ba'adin mutane da suke cewa wannan rana ta farin ciki ce. Mu wannan ranar ta bakin ciki ce saboda abin da ya samu Imam Husain",  in ji Fatima Habib daya daga cikin masu muzaharar. 

An rufe wannan muzaharar ta yau ne a daidai Kofar Kuyanbana a cikin garin Zariya ta jihar Kaduna bayan an biyo ta Kanfage, bakin kasuwa, Karauka har zuwa kan Kofar Kuyanbana. 

A cikin jawabinsa, wakilin 'yan'uwa na garin Zariya, Shaikh Abdulhameed Bello ya fara ne da mika godiya ga Allah ta'ala da ya nuna mana ranar Ashura ta wannan shekarar ta 1444. Ya ce kafin muzaharar tun farkon watan an yi zaman juyayin Ashura domin jajantawa juna; "da fadawa duniya mazalumiyar da aka yi wa jikan Manzon Allah (SAWW), Imam Husaini (AS)", inji Shehin Malamin. 

Ya ci gaba da cewa; "ga shi nan yau Allah ya ba mu dama mun fito mun yi wannan muzahara duk dai da wannan manufa na ainihin bayyanar da mazalumiya na Imam Husain (AS). Da bayyanar da matsayinmu da wulayarmu da goyon bayanmu ga iyalan gidan Manzon Allah, Muhammad (SAWW). Yadda Imam Husain (AS) ya yi yekuwa a Karbala na neman taimako da agaji, to wannan yekuwar na nan har zuwa yaumal kiyamati. Da yake cewa 'Halmin Nasirin Yansuruna'".

Har wala yau a wani bangare na Jawabinsa, Shehin Malamin ya ce; alhamdulillah da suka kasance cikin wadanda suka amsa wa Imam Husaini(AS). "kuma amsawa Imam Husaini ya nuna ainihin wulayarmu gare shi da iyalan gidansa. A lokaci guda kuma bara'a ne ga Yazidawan wancan zamani da Yazidawan wannan lokaci. Saboda haka muna kara bayyana cewa 'haihata-haihata minnaz zilla'". 

Ya kara da cewa: "kuma alhamdulillah a cikin wannan zamani Allah ya azurta mu da gwarzon jagora da ya daga ainihin tutar Imam Husaini (AS) musamman ma a wannan gari na Zariya wato Jagoranmu Sharafuddeeni Ibraheemul Zakzaky (H)". 

"Ga Yazidawa sai mu ce ainihin ba za ku ta6a nasara ba. Yadda wancan Yazidu bai samu nasara ba, kuma ba za ku samu nasara ba", ya jaddada. 

Ya kara da cewa: "yanzu ma ko a yau sun fito, tun kwana biyun nan sun fito su yi kamu a can, sun yi kamu a can, wannan ainihin wato take-take ne na ainihin kawo karshen kanku ne idan da za ku yi tunani. Wannan ba zai ta6a dakatar damu ba. Yanzu dai ga shi nan mun fito kuma ga shi nan zamu kammala muzahararmu lafiya", ya nusasshe. 

Ya lurantar da cewa: "mun sani dama sun saba,  idan an tashi lokacin da ainihin daidaikun mutane suke tafiya, sai su aukawa wasu ko su kama wasu. Saboda haka ba abin da za mu ce illa iyaka ga namu bangaren sai dai mu yi hakuri mu ma mu dauki mataki na kiyayewa. Idan an yi addu'a a kama hanya. Dama abin da ya fito damu mun zo mun yi, koma mene ne ya biyo baya mun yi nasara. Mun yi abin da ba sa so. Mun kammala kuma, to ya rage musu."

Bayan ya kammala jawabi, an yi addu'a tare da karanta ziyarar Imam Husain aka kuma sallami al'umma baki daya. 

Sai dai ganau sun shaida mana cewa; a daidai lokacin da mahalarta muzaharar ke kokarin komawa muhallansu domin ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, gamayyar jami'an tsaron Nijeriya da ya hada da soji da 'yan sanda dauke da muggan makamai harda motar yaki mai jigida sun afkama kalilan din mutanen dake kokarin komawa muhallansu da harsasai masu rai a daidai Babban Dodo. Inda suka bude musu wuta na kan mai uwa da wabi. 

Ya zuwa hada wannan rahoto, babu tabbacin adadin mutanen da aka raunata, shahadantar ko kamawa. 

No comments