Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mu Ribaci Shafukan Sada Zumunta Wajen Tallata Hajarmu

Alkaluma sun nuna cewa akalla rabin mutanen duniya ne ke ta'ammuli da shafukan sada zumunta a yau. Ke nan ga 'yan kasuwa...Alkaluma sun nuna cewa akalla rabin mutanen duniya ne ke ta'ammuli da shafukan sada zumunta a yau. Ke nan ga 'yan kasuwa za su iya fahimtar cewa wannan wata dama ce ta kulla alakar kasuwanci da al'umma mabambanta daga ko'ina a fadin duniya. 

Akwai dimbin shafukan sada zumunta da suke dauke da dabarun haduwa da al'umma da dama. Hakan na nuni da cewa akwai bukatar wadanda suke da hajoji ko wani kamfani, za su iya samar da shafin Hajarsu ko na kamfaninsu a wadannan shafukan sada zumunta domin kasancewa da masu bukatar kayayyakinsu. 

A bisa shawara, mutum ya yi la'akari da shafin da yake ganin masu bukatar kayayyakinsa za su fi kasancewa kafin ya kai ga tallatawa. 

Misali; shin kwastamominsa za su iya kasancewa a Facebook ne? Instagram, WhatsApp, Twitter ko Tiktok? A'a ko dai a YouTube ne zan samu kwastamomin da za su saya hajata? 

Fahimtar hakan na da muhimmanci ga bunkasar kasuwancinka a shafukan sada zumunta. 

Ba dole bane sai ka kasance a kowanne shafin sada zumunta wajen Tallata Hajarka, amma akwai bukatar lura kafin tsunduma a shafin da kake ganin a nan kwastamominka suke. 

©Massnoor Media Services

No comments