Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Na koma fataucin dankali saboda yajin aikin ASUU - Malamar jami'ar Nijeriya

Wata Malamar Jami’ar Uyo dake Jihar Akwa Ibom, a Kudancin Najeriya, Christiana Pam, ta rungumin sana’ar sayar da dankali domin d...Wata Malamar Jami’ar Uyo dake Jihar Akwa Ibom, a Kudancin Najeriya, Christiana Pam, ta rungumin sana’ar sayar da dankali domin daukar nauyin dawainiyarta na yau da kullum  saboda yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU. 

Tun ranar 14 ga watan Fabrairu, ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na mako hudu, amma  Kungiyar ta ci gaba da tsawaita wa'adin har sau uku wato 14 ga watan Maris, sannan ta maimaita har zuwa wasu karin makwanni 12, daga 9 ga watan Mayu domin baiwa gwamnati damar biyan dukkannin bukatun da ta gabatar.

Tsaiwata yajin aiki

A makon da ya gabata kungiyar ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da wata guda, inda ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin har sai an biya bukatun ta.

Yajin aikin a cewar kungiyar ya biyo bayan gazawar gwamnati wajen biyan wasu bukatu da suka hada da kudaden farfado da jami’o’i, wasu alawus-alawus na malaman jami’o’i, tsarin bayyana komai a jami’o’in da kuma biyan albashi da alawus-alawus na malaman jami’a, sai kuma bukatar sake sabon tattaunawa.

A wata hira da jaridar PUNCH a Najeriya malama Pam, wadda hotunan sana’arta ya mamaye shafukan sada zumunta, ta ce ta fuskanci matsalolin kudi tun a farkon yajin aikin.

Na burge wasu abokan aiki na 

Ta ce wasu daga cikin abokan aikinta sun nuna sha’awar sana’ar ta saboda rayuwa yayi tsanani saboda yajin aikin.

"Lokacin da aka kaddamar da yajin aikin na farko, na yi tunanin cewa nan da makonni hudu za a janye shi kuma za mu ci gaba da aikin mu. Na yi matukar bege da annashuwa, ina jiran a dakatar da shi amma bayan tattaunawar ASUU da Gwamnatin Tarayya, wadda har yanzu tsuguni bata kare ba, don haka aka tsawaita yajin aikin.”

Malamar Jami’ar tace ta koma gidansu a jihar Filato, kuma iyayenta duk sun yi ritaya basa aiki, sai ayyukan gona. 

Don haka na yi tunanin komawa gida Jihar Filato. Ina fama da rashin kudi har sai da na ci bashin kudi don in kai kaina wurin iyayena.”

Fatauci

Don haka, sai na fara tunanin abin da zan iya yi don samun kudin shiga don ba zan iya tambayar iyayena da suka yi ritaya kuɗi ba domin ni ya kamata na basu. Don haka, na yanke shawarar sayar da dankalin da muka girbe daga gonarmu.

Christiana Pam tace ta yi tunani mai kyau wajen fara sana’ar daukar dankalin daga Filato zuwa Uyo a jihar Akwa Ibom inda taki aiki, kuma Alhamdullillahi kwalliya na biyan kudin saboda ta zama ‘yar kasuwa.

“Iyayena sun kasance manoma tun kafin su yi ritaya, don haka bayan sun yi ritaya sun ci gaba da noma. Da na dawo gida sai na fara bin su zuwa gona da fatan bayan sati biyu za a janye yajin aikin na dawo bakin aiki amma da abin kamar wasa na fara da su wajen share gonakin, har akayi girbi ba’a janye yajin aiki ba".

©Rfi Hausa

No comments