Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijar ta musanta karbar motocin tsaro daga Nijeriya

Yayin da ake ci gaba da mahawara akan taimakon motocin yaki na naira biliyan guda da rabi da Najeriya tace ta sayawa Jamhuriyar ...


Yayin da ake ci gaba da mahawara akan taimakon motocin yaki na naira biliyan guda da rabi da Najeriya tace ta sayawa Jamhuriyar Nijar, hukumomin Nijar sun ce basu karbi wadannan motoci ba a cikin wannan shekara.

Sakataren ma’aikatar cikin gidan kasar Saidu Halilou ne ya bayyana haka, inda yace a cikin wannan shekara, gwamnatin Jihar Zamfara ce kawai ta baiwa Jihar Maradi taimakon motoci guda 5 domin samar da tsaro akan iyaka.

Hukumomin sun ce basu sani ba ko wannan taimako na kan hanyar zuwa ne, amma dai ya zuwa yanzu bai kai ga hannun gwamnatin Nijar ba.

A makon jiya ministar kudin kasar Zainab Ahmed ta shaidawa manema labarai cewar gwamnatin Najeriya ta amince da bukatar sayawa Nijar motocin da kudin su ya kai naira biliyan guda da miliyan 400 domin shawo kan matsalar tsaro.

No comments