Nijeriya na asarar Dala biyan biyu kowanne wata - NNPCGwamnatin Nijeriya ta ce, tana asarar kusan Dala biliyan biyu kowanne wata saboda satar danyan man da ake yi a yankin Neja Delta.

Shugaban kamfanin man NNPC Mele Kyari ya bayyana haka lokacin da tawagar ministan mai Timipriye Sylva ta kai ziyara ga gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a fadar gwamnatinsa da ke Asaba.

Kyari ya ce, sakamakon wannan kazamin satar da ke gudana, Najeriya ba ta iya cike gurbin da kungiyar OPEC ta ba ta na fitar da man zuwa kasuwannin duniya kowacce rana.

Kyari ya ce bayan asarar dukiyar da Najeriya ke yi, kasar kuma na fuskantar babbar matsalar gurbata muhalli a yankunan da ake satar danyan man.

Post a Comment

0 Comments