Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya na fuskantar barazanar da za ta iya rusa ta - Babban Bankin Duniya

Babban Bankin Duniya World Bank, a jiya Laraba ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar da za ta iya rusa ta. World B...Babban Bankin Duniya World Bank, a jiya Laraba ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar da za ta iya rusa ta.

World Bank ya yi gargadin cewa idan Najeriyar ta gagara gyara tsarin tara harajinta da kuma mayar da hankali akan wasu bangarorin domin bunƙasa kuɗaɗen shigarta, to ƙuɗaɗen shigarta za su ci gaba da raguwa.

Jaridar Punch ta ce wani babban jami'i a Babban Bankin Duniyar, Mr Rajul Awasthi ne ya bayyana haka a wani taro akan muhimmanci yi wa tsarin haraji kwaskwarima domin cigaban kasa, wacce wata kungiyar sa ido kan tattalin arzikin Najeriya ta shirya.

Sannan jami'in ya haƙiƙance cewa dole Najeriya ta cire rarar man fetur baki daya nan gaba.

World Bank ya bayyana cewa duk da cewa farashin man fetur na ƙaruwa a kasuwannin duniya, Najeriya ba ta samu cin gajiyar wannan dama ba saboda maƙudan kudaden da take kashewa akan rarar man fetur.

Wannan gargadi yana zuwa ne a lokacin da ƙudaden shigar Najeriya ke raguwa kuma tana cigaba da biyan tiriliyoyin nera akan rarar man fetur da matsalolin tattalin arziki.

No comments