Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Salman Rushdie Na Nan Da Ransa - Iyalinsa

Zafar Rushdie, ɗa a wurin Salman Rushdie, ya ce mahaifinsa na cikin mawuyacin hali, amma ya yi magana da iyalinsa bayan farfadow...


Zafar Rushdie, ɗa a wurin Salman Rushdie, ya ce mahaifinsa na cikin mawuyacin hali, amma ya yi magana da iyalinsa bayan farfadowarsa. Kuma tuni aka cire masa na'urar zukar numfashin da aka sanya masa. 

Wani makusancin Rushdie ya ce marubucin na cikin yanayi mara dadi matuka, amma suna fatan ya warke daga 'munanan raunukan' da aka ji masa.

Hadi Matar, matashi mai shekara 24, wanda ya sossoke Salman Rushdie, marubucin da ya yi 6atanci ga Annabi (SAWA) a wurare kusan 10 da ya hada da kai, wuya da kuma zuciya, an gabatar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da yunkurin 'kisan kai' , sai dai Hadi Matar ya musanta zargin da ake yi masa.

Alkali ya hana belin Hadi Matar, a yayin da Lauyan wanda yake kara ya yi zargin cewa an nemi hallaka wanda yake wakilta. 

Hadi Matar, bayanai sun nuna cewa ya fito ne daga Fairview, New Jersey ta kasar Amurka, an kuma haife shi ne a kasar ta Amurka. Amma iyayensa sun fito ne daga kasar Lebanon kamar yadda jami'an Lebanon suka shaidawa kafafen watsa labarai. 

Kafar watsa labaran NBC dake Amurka, ta ce Hadi Matar yana goyon bayan manufofin rundunar Soji ta IRGC ta jamhuriyyar Musulunci ta kasar Iran. Amma sun ce babu wata kwakkwarar shaida dake nuna alakar dake tsakanin Hadi Matar da IRGC din.

No comments