Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Hausawan Agege Ya Bai Wa Farfesa Abubakar Gwarzo Sarautar ‘SO DANGIN AGEGE’

    Sarkin Hausawan Agege da ke jihar Legas, Alhaji Musa Muhammad Dogon Kadai, ya bai wa wanda ya assasa kuma shugaban majalisar gudanarwa...

 


 Sarkin Hausawan Agege da ke jihar Legas, Alhaji Musa Muhammad Dogon Kadai, ya bai wa wanda ya assasa kuma shugaban majalisar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo sarautar “So Dangin Agege”.

An bayar da sanarwar bayar da Sarautar ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Mai Martaba Sarkin Hausawan Agege a Legas, Alhaji Musa Muhammad Dogon Kadai a ranar Asabar, 13 ga watan Agusta, 2022 kuma aka mika wa Farfesa Gwarzo.

Takardar ta ce an zabi a bai wa Farfesa Abubakar Gwarzo wannan sarautar ne a yayin taron majalisar zartarwa na karshe a kan tarihin masarautar al’ummar Hausawan Agege.

A cewar wasikar, Farfesa Abubakar Gwarzo ya cancanci wannan nadin duba da kyawawan halayensa na shugabanci.

A cikin wasikar da Majalisar Masarautar ta fitar ta kuma mika wa Farfesa Gwarzo a ranar 10 ga watan Agusta, 2022, ta bayyana irin gudunmawa mai gudana, jajircewa da kuma sadaukarwar Farfesa Gwarzo a matsayin abin koyi.

“Farfesa Gwarzo mutum ne da a ko da yaushe yake nuna damuwa da sadaukar da kai ga ci gaban al’ummar masarautar Agege baki daya,” in ji wasikar. 

Majalisar Masarautar ta yabawa Gwarzo bisa irin hidimar da yake yi wa al’umma, sannan ta yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi masa albarka, ya yi masa jagoranci, sannan ya kuma ba shi hikima da jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora masa kamar yadda aka yi tsammani.

 No comments