Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jajanta wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa

 Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa al’ummar jihar Kano musamman wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.  A ... Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa al’ummar jihar Kano musamman wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.


 A wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Sarkin ya bayyana alhininsa game da ambaliyar ruwa da aka gani a wasu sassan jihar.


 Sarkin ya yi kira ga al'uma da su guji zubar da shara a hanyoyin ruwa domin kaucewa afkuwar lamarin nan gaba.


 Alhaji Aminu Ado Bayero ya jaddada bukatar malamai su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai domin magance matsalolin ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar rasa matsuguni da asarar dukiyoyi.


Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano.

 30/8/2022

No comments