Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sha'awar Ilimi Daga Zuciyata Yake – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sha’awarsa ga ilimi ta fito ne daga zuciyarsa.   Atiku ya bayya...


Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sha’awarsa ga ilimi ta fito ne daga zuciyarsa. 

Atiku ya bayyana hakan ne bayan kaddamar da makarantar Atiku Abubakar ta ilimin zamantakewa da gudanarwa a jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke jihar Kano a yau Laraba.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya ce kaddamar da wannan makaranta wani muhimmin abu na ziyarar da ya kai jihar.

Atiku ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Abin farin ciki ne na kaddamar da Makarantar Koyon Zamantakewa da Gudanarwa ta Atiku Abubakar a Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke Kano a yau. Wannan kuma wani babban al'amari ne na ziyarata a Kano.

"Sha'awata kan ilimi ya fito ne daga cikin zuciyata da kuma irin tasirin da hakan ya yi a tsawon rayuwata”, inji shi.

Daga cikin wadanda suka yi wa Atiku Abubakar rakiya akwai; mataimakin dan takarar shugaban kasa a PDP din, Ifeanyi Okowa, Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, Sanata Ibrahim Shekaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da sauran su.

 

No comments