Shari'ar zaben kujerar Dan Majalisar Dattijai a mazabar shugaban jam'iyyar APC ta kasa tana kara zafi. Shari'ar wand...
Shari'ar zaben kujerar Dan Majalisar Dattijai a mazabar shugaban jam'iyyar APC ta kasa tana kara zafi.
Shari'ar wanda Barista Labaran Shu'aibu Magaji ya shigar yana kalubalantar nasarar Arc. Shehu Tukur kan zaben fidda gwani da ya gudana a ranar 4/6/2022 wanda ya ce tana cike da almundahana.
Tuni dai Alkalin Kotun Gwamnatin tarayya dake zamanta a Lafia, mai shari'a Nehizina Idumudia Afolabi ta fara sauraren karar tun a watan jiya.
A ranar Laraba 3/8/2022 Lauyoyi sun ci gaba da tada jijiyoyin wuya da musayan kalamai domin kare wadanda suke wakilta.
Sai dai abubuwan da ya daurewa mai shari'an kai a zaman da aka yi a ranar Laraba yayin da Layoyin Labaran Magaji suke kalubalantar nasarar Shehu Tukur a matsayin an sauyo sunayen masu zaben 'yan takara a karamar Hukumar Keffi da Nasarawa.
Suka ce takardar da asalin sunayen masu zaben na asali yake an sauya, an yi amfani da wani takarda da sunaye na daban.
Mai shari'ar Nehizina Idumudia Afolabi ta bukaci a zo da wakilin Hukumar zabe (INEC) da ya gudanar da zaben fidda gwani a ranar.
Sakamakon takardar dake dauke da bayanan masu zaben akwai sabanin sanya hannu daban-daban.
Tuni ta bukaci da Mr Omale Samuel ya kawo kansa gaban Shari'a a ranar 31/8/2022 domin bambance asalin sanya hannunsa cikin takardun.
A nasa jawabin Barista Labaran Shuaibu Magaji ya ce yana da tabbacin zai yi nasara a wannan shari'ar. Domin gaskiya za ta yi halinta.
Ya kara jaddada cewa yana tara da Jam'iyyar APC yana tara da Gwamna Abdullah Sule.
A nasa jawabin Barista Gali Umar Ahmed ya ce; muna da hujojin da za su tabbatar mana da nasara cikin wannan shari'ar.
Yanzu ga shi Kotu ta fara gayyatar mutanilen da suka sauya al'amuran da su zo su kare kansu.
Ya ce; muna da hujoji da sunayen masu zaben Dan takara na asali da jabun da aka yi amfani da su.
Zuwan Mr Omale Samuel zai kara tabbatar da gaskiyar maganar da muke yi, na cewa an yi amfani da sunayen mutanen da babu sunansu a cikin masu zaben.
Barista Gali ya ce,; muna jiransu mu hadu ranar.
Shima Barista Ibrahim Bawa mai kare jam'iyyar APC ya ce; Kotu ta bukaci Ma'aikacin Hukumar zaben Mr. Omale Samuel da ya gurfana gabanta saboda bambanci sanya hannaye a kan takardun zaben.
Ya ce; shari'a mace ce mai ciki ba a san mai za ta haifa ba. Amma yana fatan a gudanar da shari'ar lafiya a gama lafiya.
Shima Lauyan wanda ake karar ya ce suna da cikakken hujojin da za su gabatar ma kotu cewa sun yi nasara.
No comments