Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shekaru 9 a Tsare: Harkar Musulunci ta yi kira da a saki Haruna Abbas, da wasu mutane biyu

An yi kira ga mahukuntan Najeriya da su kawo ƙarshen ci gaba da tsarewar da ake yi wa wasu mutane uku cikin Almajiran Sheikh Ibr...An yi kira ga mahukuntan Najeriya da su kawo ƙarshen ci gaba da tsarewar da ake yi wa wasu mutane uku cikin Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky da suke tsare kusan shekaru tara.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mohammad Abdullahi a madadin yan uwan ya nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da tsare Almajiran Shehin Malamin ba tare da ƙa'ida ba bayan azabtarwa.

Sanarwar ta ce, “Shekaru 9 ke nan da hukumar DSS ta kama Malam Haruna Abbas da Ibrahim Hussain da kuma Adamu Suleiman ba bisa ka’ida ba a filin jirgin sama na Aminu Kano a ranar 16 ga wata da Malam Harunan ya fito daga kasar waje, a watan Maris kuma 2013. An kama Ibrahim Hussaini da Adamu Suleiman a mazauninsu a cikin danginsu.

“Bayan kama shi, an kai Haruna Abbas hedikwatar DSS ta kasa da ke Abuja, kuma an killace shi na tsawon kwanaki 3 tare da yi masa tambayoyi daga jami’an MOSSAD. Ana Tuhumar Malam Haruna ne da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci ta hanyar aika Ibrahim da Adamu zuwa kasashen waje domin samun horon ta’addanci a cikin jerin tambayoyin da ake yi masa. 

“Bayan shafe sama da shekaru 2 a hannun DSS, sai hukumar ta mayar da wadanda aka tsare zuwa gidan yari. An kai waɗanda aka kama zuwa Kotu a ƙarƙashin kotun Mai shari’a Ademola wanda daga bisani aka sake mayarwa wajen mai shari'a Chikere har yanzu ana ta canza salo daban-daban. 

Abdullahi ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake tsare da su, Haruna Abbas na fama da matsalar hawan jini, ciwon suga da sauran matsalolin irin na rashin lafiya.

Yayin da yake zargin  tsoma bakin ƙasashen waje su Amurka da gwamnatin Isra'ila ke yi, akan shari'ar ya ce kokarin da ake na neman belinsu a lokuta daban-daban abun ya ci tura.

No comments