Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Izala, Alhaji Bala Lau Ya Samu Kwantiragin Tsaro Na Fiye Da Naira Miliyan 400 Daga Gwamnatin Tarayya

Daga Muhammad A. Dalhatu Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; a ranar Larabar 25 ga watan Agustan 2022, Kwamitin zartaswa ta gwamna...


Daga Muhammad A. Dalhatu

Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; a ranar Larabar 25 ga watan Agustan 2022, Kwamitin zartaswa ta gwamnatin Tarayya da ake ce ma FEC, ta amince da a bayar da Kwantiragin tsaron titunan jiragen kasa na Abuja da ake ce ma 'Abuja Rail Mass Transit' a turance a matakin farko (Lots 3 da 1A) akan kudi naira miliyan dari bakwai da sha takwas da dubu dari da casa'in da uku da dari biyu da hamsin (718, 193, 250). 

Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello  ne ya tabbatar da hakan, jim kadan da kammala zaman Majalisar zartaswar ta gwamnatin Tarayya  a fadar shugaban kasa dake Abuja.

An bayar da Kwantiragin tsaron ne ga kamfanuka guda biyu da ya hada da Al-Ahli Security Guards Ltd akan kudi naira miliyan dari hudu da bakwai da dubu dari biyu da sha hudu (407, 214, 000) wanda za su kula da akalla titin kilomita 27. 245 wanda ya hada tasohin jiragen kasa guda takwas.


Sai kuma kamfanin Segad Security Protective Company Ltd akan naira miliyan 310, 979, 250 wanda zai lura da kilomita 18 a tasoshin jiragen kasa hudu.

Kwantiragin na tsawon shekaru biyu ne kacal; wanda tsawon shekarun nan, kamfanukan biyu za su lura da hanyoyin layin dogo, samar da ababen more rayuwa ga cibiyar sadarwa, da sarrafawa na jirgin da kuma na'u'rorin hasken lantarki da kuma sigina. 

Sai dai bayanan da wakilinmu ya bincika a shafin Intanet na hukumar yi wa kamfanuka rijista ta Nijeriya wato CAC, ya nuna cewa wani mutum ne mai suna Abdullahi Alhaji Bala Lau ne mallakin kamfanin.


Shafin ya ce Abdullahi Alhaji Bala Lau yana zaune ne a No. 1 Junction Wukari Street, Jimeta Yola dake jihar Adamawa. Sai dai kamfanin na da adireshin mai lamba 2 Kofare Industrial Layout, Opposite Adama Plast. Off Numan Road, Jimeta Yola a jihar Adamawa.


Sai dai bayanai a shafin Intanet da wakilinmu ya bincika sun tabbatar da cewa Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar JIBWIS bangaren Kaduna, shi ne kadai fitacccen mutumin da ke da wannan suna.

Sannan wata majiyarmu a Yola ta tabbatar mana da cewa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ke da kamfanin tsaron na Al-Ahli Security Guards Ltd. Sannan adireshin da CAC suka buga, adireshin gidansa ne dake Yola ta jihar Adamawa. 

Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Sheikh Abdullahi Bala Lau, abin ya ci tura.  Domin bai same shi a waya ba. 

No comments