Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban MAAUN Nijeriya Ya Kai Ziyarar Godiya Ga Mai Martaba Sarkin Kano

Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr a ranar Laraba, ...


Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr a ranar Laraba, 10 ga watan Agusta, 2022 ya kai ziyarar godiya ga Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero bayan da Sarkin ya kai ziyarar ban girma ga jami’ar.

Farfesa Israr ya samu rakiyar mataimakin shugaban jami’ar bangaren gudanarwa kuma Magatakardar MAAUN Nijar da Dakta Shu’aibu Tanko da kuma Daraktan hadin gwiwa da kulla alaka na MAAUN, Dakta Bala Muhammad Tukur da wasu jami’an jami’ar zuwa fadar Sarkin.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Farfesa Israr ya bayyana jindadinsa da ziyarar da Mai Martaba Sarkin Kano ya kai MAAUN Kano tare da rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da bai wa Sarkin lafiya da basira domin daukaka masarautar ta Kano.

“A madadin hukumar gudanarwa, wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, muna mika godiya ga Mai Martaba bisa irin karramawar da aka yi wa jami’ar,” inji shi.

Da yake mayar da jawabi, Mai Martaba Sarkin Kano wanda ya yi magana ta bakin Makaman Kano, Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim ya bayyana farin cikinsa da ziyarar ta godiya.

Ya kuma nuna jindadinsa kan kayayyakin da ya gani a lokacin da ya kai ziyarar ta fahimtar juna a MAAUN Kano a ranar Litinin.

Ya ce Masarautar ta yaba wa wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa jami’ar a Kano.

A don haka ya yi kira ga masu hannu da shuni a cikin al’umma da su yi koyi da Farfesa Gwarzo ta hanyar kafa irin wannan jami’a domin ci gaban ilimi a jihar da ma kasa baki daya.

No comments