Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Talaka ne zai ji a jikinshi idan aka kara wa kamfanoni haraji a Najeriya - ALTON

A Najeriya, gwamnatin kasar ta tabbatar cewa tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kan batun wani karin harajin cikin gida da k...


A Najeriya, gwamnatin kasar ta tabbatar cewa tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kan batun wani karin harajin cikin gida da kashi biyar cikin 100 nan gaba.

Masu sharhi kan tattalin arziki a kasar na ganin yunkurin wani kokari ne na samar da karin kudin shiga ga aljihun gwamnati, yayin da tattalin arzikinta ke kara fuskantar kalubale.

Masana fannin tattalin arzikin irin su Dokta Shamsudeen Muhammad, na Jami'ar Bayero da ke Kano, na ganin wannan karin haraji da gwamnatin Najeriya ke tunanin yi, a zahiri take neman karin kudin shiga take yi.

Kuma a cewarsa hakan ba laifi bane ko kuma wani sabon abu, sai dai matsaloli ka iya tasowa nan gaba a dalilin karin.

' Shi wannan harajin yana da nasa illolin ga tattalin arzikin kasa da kuma walwalar 'yan kasa gaba daya.''

'' Irin wannan haraji idan an daura wa kamfanoni ba wai kamfanonin ke biya ba. Suma kamfanonin suna kara farashin kayayyakinsu ne daidai da abunda aka dora musu na haraji.''

'' Kenan talakawan da suke kwastomominsu suke sayen kayansu sune za su biya wannan harajin, kuma idan aka yi haka lamarin zai kara hauhawar farashi a Najeriya,'' in ji Dr Shamsuddeen.

BBC ta tuntubi Malam Yunusa Tanko, mataimaki na musamman ga ministar kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmad, wanda ya tabbatar mata da cewa ana muhawara tsakanin masu ruwa da tsaki, domin duba yiwuwar bullo da karin harajin ga kamfanoni nan gaba a kasar.

 To amma ya ce har sai an cimma maslaha game da batun, sannan ma'aikatar kudin Najeriyar za ta iya karin haske kan batun aiwatar da sabon harajin.

 Sai dai yayin da ma'aikatar kudin ta Najeriya ke wannan bayani, tuni wasu daga cikin wadanda harajin zai shafa suka fara bayyana matsayarsu, idan ma an bullo da karin harajin.

Sai dai yayin da ma'aikatar kudin ta Najeriya ke wannan bayani, tuni wasu daga cikin wadanda harajin zai shafa suka fara bayyana matsayarsu, idan ma an bullo da karin harajin.

Gbenga Adebayo, shine shugaban kungiyar masu harkokin sadarwa a Najeriya ta Alton, ya kuma ce sam ba su shirya rungumar sabon haraji ba a yanayin da kasuwancinsu ke tafiya.

Ya kara da cewa idan ma haka ne a kan masu amfani da kayansu abun zai kare, kamar yadda masu sharhi kan tattalin arziki ke hasashe.

 ''Ba za mu iya daukar nauyin wannan haraji a madadin masu amfani da waya ba, saboda haka za mu mayar da shi ne kai tsaye gare su, wato dai za mu rika cire shi ne daga cikin katin waya da sukan saya, kana mu mika abin da muka tara ga gwamanti, in ji Adebayo.''

 Ya kara da cewa ''za ka ga aukin katin da ka sa na waya ko kiran da za ka yi ya ragu, alal misali idan ka sayi katin naira 100 ko 1000, za ka ga cewa aukinsa ya ragu da kashi biyar cikin 100. Saboda haka, mu ba za mu kara kudin amfani da waya ba.''

Batun harajin da gwamnatin Najeriyar ke tattauna yiwuwar karawa nan gaba, yana zuwa ne yayin da kasashen duniya da dama ke kokarin kirkiro karin hanyoyin samun kudaden shiga, sakamakon yadda tattalin arzikin duniya ke fuskantar kalubale ta fuskoki daban-daban a yan shekarun nan.


-BBC HausaNo comments