Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tarar Naira Miliyan 5 ga Trust TV Kan Hira da Ƴan Bindiga: Shin Ƴan Jarida Ina Zamu sa Kanmu?

Daga Comrade Yahaya M Abdullahi Bazan ma fara rubutun ba sai nayi dogon jinjinar ban girma ga mai gidanmu abun koyi a aikin jari...Daga Comrade Yahaya M Abdullahi

Bazan ma fara rubutun ba sai nayi dogon jinjinar ban girma ga mai gidanmu abun koyi a aikin jarida Malam Abdulaziz Abdulaziz bisa wannan jajircewa da sadaukar da rayuwarsa da yayi domin binciko gaskiya akan ƴan ta'adda tare da bayyana ta ga al'umma, wannan kuma shine asalin Haƙiƙanin aikin jarida da ma'anar Ɗan Jarida. Ba wai kawai iya kare muradin Gwamnati mai ci bane aikin jarida kamar yanda wannan Gwamnatin ta Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari take so ayi.

Maganan gaskiya na nemi tattaunawa da Bello Turji tun kafin malam Abdulaziz yayi wannan hirar da ni da wani abokina ana ce masa Ajayi, wanda yake aiki da gidan talabijin na 'African News' amma lamarin ya ci tura, nasan waɗanda suka san na musu magana suna da yawa duk da ita inda zamu hi mu samu damar hakan mun rasa sai dai kawai alƙawura da muka samu wanda kuma ba su samu damar cika ba. Ganin hirar da 'Trust TV' tayi da waɗannan ƴan Ta'adda yasa na jinjina sosai musamman ga wanda ya sadaukar har hirar ta zo mana.

A hirar lallai akwai abubuwan dubawa sosai musamman ga duk wanda ya saurari zantukan dake fitowa daga bakin shi ƙasurgumin Ɗan Ta'addan kamar yanda ya kira kansa da kansa wato #Bello Turji, daga ciki kuwa harda maganan siyasa, wannan shine babban abun dubawa da kuma lamarin ajiye makamin da suka ce zasu yi domin su rungumi sulhu saboda mutanen da ake kashewa abun ya yi yawa, kuma lallai ga duk mai hankali yasan lallai maganan Turji shine gaskiya, to amma da yake ita Gwamnatin yin hakan shine yake basu damar samun kuɗi da ci gaban mulkinsu sam hakan bai ɗaɗarasu da ƙasa ba, kawai abunda ya fi damunsu shine waɗanda suka yi Hirar.

A Najeriya babu wanda bai san cewa Gwamnatin da aka zaɓeta da gagarumin ƙuri'u mafi rinjaye domin ta kare rayukan ƴan ƙasa da dukiyoyinsu ta gaza ba musamman ta hanyar yin ƙarairayi akan matsalar tsaro, a koda yaushe idan suka fito zasu ce an bada izinin a nemo inda ƴan ta'adda suke domin maganinsu alhalin kuma an san inda suke domin ga Ɗan Jarida ya binciko, in dai Ɗan Jarida da aka sani da labari zai san inda ƴan ta'adda suke ina ga kuma waɗanda ake basu maƙudan kuɗaɗen a koda yaushe domin bincike da magance matsalar tsaro? 

Ba kawai iya Ƙalubalen matsalar tsaro muke fuskanta a ƙasar nan ba, harma da ƙalubalen barazana da yanka tara ga duk wanda ya Faɗi gaskiya. Wannan Gwamnati ta Shugaba Buhari me yasa a koda yaushe ta zama jaruma wajen takura da hana faɗin albarkacin baki, ba iya nan bama har ma da masu taimakonta take su take domin abunda trust TV tayi taimaki ne ga Gwamnati, to amma saboda ba aiki suke so ba dole ya zamanto an yanka musu tara su biya, kai kace su basu yi zama a jam'iyyar Adawa ba, wanda da Ace Malam Garba Shehu da Malam Lai Mohammed za'a dawo musu da rubuce-rubucen da suka aika a zaman mulkin shugaban ƙasa Jonathan kamata yayi su rataye kansu saboda kunya da irin cin mutunci da zarafin da suka yi ma Gwamnatin da alƙalumansu da kuma bakunansu a gidajen talabijin da rediyo, to amma sai gashi yanzu sun mance, tir da hakan.

Nitional Broadcasting Commission (NBC) ya kamata ku gane cewar hada kai da Gwamnati domin takura ma waɗanda ke ƙarƙashin kulawarku ba inda zai kai ku sai asara, ita Gwamnatin da ta saka ku yin hakan kwanaki nawa suka rage mata? Ku kuwa fa kuna nan muma muna nan, tarihi zai taskance abunda kowa ya aikata, kun yanke ma #Channelstv tarar miliyan biyar kwanakin baya, yanzu ma kun yanke ma trust TV, duka saboda kuma fadan gaskiya, in kuma akwai inda suka yi laifi ko karya doka sai a kawo a rubuce kamar yanda doka ta tanadar, amma wata rana sai labari.

Ina jinjina na musamman ga kamfanin Trust, Allah ya ƙara hazaƙa, in dai Gwamnati ba tana tare da ƴan bindiga bane, kuma in dai yan Bindiga ba ma Gwamnatin suke yi wa aiki ba to lallai abunda kuka yi ɗin nan ya fito da komai fili tas, ya kamata a jinjina muku tare da ɗaukar Mataki ne na tsaro akan yan Ta'adda ba Yan Jarida ba.


#JinjinagatrustTV
#AikinJaridabaTaaddancibane

Comrade Yahaya M Abdullahi, Ɗan Jarida kuma Marubuci, za'a iya samunsa a 07033800660 ko Comradeyahaya20@gmail.com

No comments