Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yajin Aiki: Ba Za Mu Biya Malaman Jami'a Albashi Ba - Gwamnatin Nijeriya

  A wani lamari mai kama da karfa-karfa da danniya ga Malaman Jami'a, gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, babu gudu babu ja da baya danga...

 


A wani lamari mai kama da karfa-karfa da danniya ga Malaman Jami'a, gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce, babu gudu babu ja da baya dangane da aniyarta ta kin biyan malaman jami’oin da ke yajin aiki albashinsu na watanni 5 da suka gabata, saboda kin koyar da yara a makarantu.

Ministan ilimi Adamu Adamu ya ce, wannan matsayi da suka dauka shi ne ya hana cimma yarjejeniyar janye yajin aikin da yanzu haka ya wuce watanni 6.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa, ministan ya ce kungiyar malaman ta ki kiran mambobinta su koma bakin aiki ne saboda kin amincewa da bukatar a biya su daukacin albashinsu na watanni 5 da suka kwashe suna yajin aikin.

Adamu ya ce bangarorin biyu sun amince tare da cimma yarjejeniya akan batutuwa da dama da aka gabatar a tattaunawar da suka yi, yayin da 4 daga cikin kungiyoyi 5 na ma’aikatan jami’oin suka amince su janye yajin da suke yi nan da mako guda mai zuwa bayan gudanar da taron shugabanninsu na kasa.

Dangane da batun biyan dalibai hakkinsu na watanni da suka kwashe a gida suna zama lokacin yajin aikin kuwa, ministan ya ce, wannan ba hurumin gwamnati ba ne, sai da malaman da suka tafi yajin.

Adamu ya ce daliban na da hurumin zuwa kotu domin neman fansa daga malaman.

No comments