Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Yakamata Gwamnatin Jihar Edo Ta Yi Mana Adalci, Inji Sarkin Sarakunan Fulanin Jihar Edo

Daga Idris Umar Sarkin Sarakunan Fulanin jihar Edo Alhaji Muhammadu Sosal yayi kira ga gwamnatin jihar Edo da ta yi wa Allah da ...


Daga Idris Umar

Sarkin Sarakunan Fulanin jihar Edo Alhaji Muhammadu Sosal yayi kira ga gwamnatin jihar Edo da ta yi wa Allah da Annabinsa ta janye dokar da tasa na korar Fulani a jihar baki daya nan da kwana biyar

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai akan hukuncin kwana 5 da kwamitin taba kowanne Bafullatani ya bar jihar.

Sarki ya ce a gaskiya daukar wannan mataki zai cutar da Fulanin dake zaune a dukkan fadin jihar bisa ga yadda mafi yawan filanin dake zaune a jihar sun haura shekaru 30 zuwa 50 suna zaune a jihar ba tare da an same su da wani laifi ba.

Basaraken ya ce mai zai hana a gaya masu laifin da sukayi kafin a kore su.

Sannan ya tabbatar da cewa su ba sa marawa duk wani batagarin Fulani baya, kuma ba su yadda da ta'addanci ba kuma suna goyan bayan hukunta duk wanda ya yi laifi.

Tuni Sarkin ya janyo hankalin gwamnati da su ba su damar saurarensu mai makon ba su kwana biyar musamman a irin wannan yanayin mai cike da kalubale.

Shugaban ya ce; "Ina da tabbacin duk inda muka je babu wanda zai yarda da mu saboda yanayin da ake ciki na rashin aminci"

Ya ce don haka yana son a saurare su don su ji dalilin korar ta su bayan da yawan Fulani suna da gonaki da suka yi shuka kuma amfani ya yi girma dosai.

Kuma ya ce su a gare su jihar Edo jihar sune tunda da yawansu a nan aka haife su. 

Bisa haka Sarkin ya ce yana kira ga gwamna da duk sauran masu fada a ji su sa baki don gyara lamarin ya ce ba dukan Fulani suka zama lalatattu ba akwai masu tsoran Allah da kiyaye doka.

Ya ce yanzu haka suna da labarin an fara kona wasu gidaje a wasu yankin bisa haka Sarkin ya nemi gwamnati ta duba wannan lamarin don daukar mataki.

No comments