Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YAKI DA RASHAWA: Buhari Ba Da Gaske Ya Ke Ba, Cewar Naja’atu Muhammad

Sananniyar ‘yar Siyasar nan ta jihar Kano kuma mamba a kwamitin ɗauka da ladabtar da ‘Yan sanda Naja’atu Mohammed, ta caccaki Sh...


Sananniyar ‘yar Siyasar nan ta jihar Kano kuma mamba a kwamitin ɗauka da ladabtar da ‘Yan sanda Naja’atu Mohammed, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

A wata tattaunawa da Radio France International, RFI a ranar Litinin, wacce Daily Nigerian ta saurara, Najaatu Mohammed ta ce ya dace Buhari ya gane cewa dukiyar Najeriya ba ta shi bace. A jiharsu ya dace a yafe musu in ji ta, ya kamata gwamnonin jihohinsu su yafe musu ne, saboda acan suka aikata rashawar, don kundin tsarin mulki ya bayar da yafiya ne ga jihohin da aka aikata laifuka.

Ta kara da cewa yafe wa tsofaffin gwamnonin yana nuna cewa ba a shirya kawo karshen rashawar Najeriya ba. Ta ce kotu ta tabbatar da zargin da ake musu don haka yafiyar na nuna cewa ba a yaki da rashawa a kasar nan.

“Gwamnati ta yi kuskure. Ya dace shugaban kasa ya gane cewa dukiyar al’umma ba ta shi bace. Gwamnatin tarayya ba ta da damar yafe wa wadanda suka tafka laifi a jihohinsu. “Abu na biyu shi ne wannan yafiyar ta Buhari tana nuna cewa gwamnati ta gaza.

“Bayan EFCC da kotu sun gama iyakar kokarinsu tsawon shekaru, bai dace kawai ka yafe wa masu laifin ba. Ba kudinka suka sata ba. Me yasa gwamnatin Buhari ta ke yin yadda ta ga dama?”

Ta ce a tarihin Najeriya ba a taba mulki mai rashawa da sata kamar na mulkin Buhari ba A cewarta kundin tsarin mulki bai bayar da damar yin wannan haukar ba. Idan haka ne ya kamata a yafe wa ‘yan ta’adda. Saboda babu ta’addancin da ya zarce satar da gwamnonin suka yi.

No comments