Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Nassarawa

Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace kwamishinan labarai, al'adu da yawon bude ido, na Jihar Nasarawa, Mallam Ya...Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace kwamishinan labarai, al'adu da yawon bude ido, na Jihar Nasarawa, Mallam Yakubu Lawal. 

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan bindigan sun sace Lawal ne a gidansa da ke Nasarawa Eggon a daren jiya Litinin bayan sun yi harbe-harben bindiga. 

 Wata majiya daga iyalan kwamishinan, wanda ba ta son a ambaci sunanta, ta tabbatar da afkuwar lamarin. 

Majiyar ta ce yan bindigan da suka yi awon gaba da kwamishinan suna dauke da muggan makamai masu yawa.  

An yi kokarin tuntubar mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa domin ji ta bakinsa amma ba a same shi ba zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A ƴan kwanakin nan, karamar hukumar ta Nassarawa Eggon na fama da hare-haren ƴan bindiga. 

Ko a ranar Asabar din nan da ta gabata sai da Yan Bindiga suka kashe wani malami  makarantar  sakandiren gwamnati ta kimiyya da ke karamar hukumar ta Nasarawa Eggon. 

No comments