Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Sanda Sun Kama Mace Da Zargin Kashe Mijinta A Jihar Kebbi

  Rundunar 'yan sanda reshen Jihar Kebbi a arewacin Najeriya ta ce ta kama wata mace mai shekara 30 bisa zargin kashe tsohon mijinta, wa...

 


Rundunar 'yan sanda reshen Jihar Kebbi a arewacin Najeriya ta ce ta kama wata mace mai shekara 30 bisa zargin kashe tsohon mijinta, wani alƙalin kotun majistare mai suna Attahiru Ibrahim Zagga.

Kakakin rundunar, SP Nafiu Abubakar, ya faɗa wa BBC Hausa cewa da misalin ƙarfe 9:00 na dare ranar Alhamis ne maƙota suka kai musu rahoton cewa sun ji hayaniya a gidan alƙalin da ke unguwar Alieru a birnin Kebbi.

Da isar jami'ansu ne kuma suka tarar da Attahiru kwance cikin jini, inda suka garzaya da shi asibita kuma a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

"Bayan shigar jami'anmu gidan suka tarar da tsohuwar matarsa mai suna Farida Abubakar kuma aka kama ta da zargin hannunta a aikata kisan," in ji SP Nafiu.

Kafin mutuwarsa, Attahiru Ibrahim alƙalin kotun majistare ne a garin Jega na Ƙaramar Hukumar Jega.

No comments